Zaben Edo: Rigima Ta Barke a Rumfar Zabe, INEC Ta Manta da Takardar Rubuta Sakamako

Zaben Edo: Rigima Ta Barke a Rumfar Zabe, INEC Ta Manta da Takardar Rubuta Sakamako

  • An dakatar da kada kuri'a a wata rumfar zabe da ke gundumar Orhionmwon da ke a karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo
  • An ce matasan rumfar ne suka tayar da rigima bayan da suka gano jami'an INEC ba su zo da takardar rubuta sakamakon zaben ba
  • Wani bdiiyo da Legit Hausa ta gani ya nuna yadda matasan suka dage kan cewa har sai INEC ta gabatar da takardar za a ci gaba da zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Sabuwar rigima ta barke a gundumar Orhionmwon da ke karamar hukumar Orhionmwon ta Edo yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar.

An rahoto cewa yanzu haka an dakatar da kada kuri'a a rumfa ta daya a gundumar bayan jami'an INEC sun manta da takardar rubuta sakamakon zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Wakilan APC da PDP na ba masu kada kuri'a cin hancin N10000’

Edo: Mutane sun tayar da tarzoma a rumfar zabe bayan INEC ta manta da takardar rubuta sakamako
Zaben Edo: Masu kada kuri'a sun hargitsa runfumar zabe saboda rashin takardar sakamako.
Asali: Twitter

An dakatar da kada kuri'a

Wani bidiyo da jaridar Leadership ta wallafa ya nuna yadda ake hargitsi a rumfar zaben, inda aka ji matasan wajen na cewa ba za a ci gaba da kada kuri'a ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anji wani ya na cewa "Babu takardar sakamakon zabe babu kada kuri'a" yayin da wani ke cewa "ta ya ya za su zo rumfar zabe babu takardar rubuta sakamako?"

Matasan sun dage kan cewa ba za su amince da zaben ba ma damar jami'an hukumar INEC suka gaza gabatar da takardar rubuta sakamakon zaben rumfar ba.

Matashi ya fadi abin ke faruwa

Wani matashi da ya tsaya gaban bidiyon, ya yi bayanin cewa jama'ar rumfar sun fara kada kuri'unsu amma daga bisani suka gano cewa babu takardar rubuta sakamako.

"Ta yaya za su samu mu fara kada kuri'a alhalin sun san ba su zo da takardar rubuta sakamako ba? Da ma haka ake gudanar da zaben ne?

Kara karanta wannan

Edo 2024: INEC ta tsawaita lokutan zabe, ta fadi musabbabin ɗaukar matakin

"Ba zamu lamunci haka ba. Ba mu ci gaba da kada kuri'a ba har sai sun nuna mana takardar da za su rubuta sakamakon zaben."

Bidiyon dai ya nuna dandazon masu kada kuri'ar da suka hada da maza da mata, manya da samari wadanda suka yi cirko cirko a kan layi.

Kalli bidiyon a kasa:

EFCC ta kama masu sayen kuri'a

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa jami'an hukumar EFCC sun cafke wasu mutane uku da ake zargi suna sayen kuri'u a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.

An rahoto cewa EFCC ta cafke mutanen da suka hada da maza biyu da mace daya, sai dai kuma wasu mutane da ke wajen sun nuna adawa da matakin da hukumar ta dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.