"Ko Nawa ne": Kwamishinar Zabe a Edo Ta Magantu kan Karbar Rashawa, Ta Fadi Shirinta

"Ko Nawa ne": Kwamishinar Zabe a Edo Ta Magantu kan Karbar Rashawa, Ta Fadi Shirinta

  • Yayin da aka fara kada kuri'a a zaben jihar Edo, kwamishinar zabe ta bayyana shirin hukumar domin yin adalci
  • Farfesa Rhoda Gumus ta ce ko nawa aka kawo mata na cin hanci ba za ta taɓa karba ba domin kare mutuncinta
  • Farfesa Gumus ta ce ko kusa babu wanda ke da karfin halin da zai tunkare ta game da cin hanci ko biliyan nawa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Kwamishinar hukumar zabe a jihar Edo ta yi magana game da karbar cin hanci.

Farfesa Rhoda Gumus ta sha alwashin kin amincewa da duk wani tayin cin hanci da za a bata komai yawansa.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da za su iya jawo jam'iyyar PDP ta faɗi a zaɓen gwamnan jihar Edo

Hukumar INEC a Edo ta sha alwashi game da karbar cin hanci
Kwamishinar zabe a Edo, Farfesa Rhoda Gumus ta ce ba za ta taɓa karɓar cin hanci ba. Hoto: Prof. Rhoda Gumus.
Asali: Facebook

Edo: Kwamishinar zabe ta magantu kan rashawa

Rhoda ta bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a daren jiya Juma'a 20 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesar ta bugi kirji inda ta ce babu wanda ke karfin hali da zai tunkare ta da maganar cin hanci saboda mutuncinta.

Ta yi alkawarin cewa zaben jihar Edo zai zamo mafi kyawun zabe da hukumar INEC za ta gudanar a Najeriya.

"Ni nake kula da jihar Edo, zan yi abin kirki duk da ba zan kasance a ko ina ba, za mu tabbatar da yin zaɓe cikin adalci."
"Ba zan karbi cin hanci ba ko nawa ne, ba na bukatar karbar biliyoyi domin yin abin da ya dace."
"Babu wanda ya isa ya gwada hakan a kai na, bai isa ba, idan kana da ofis a Najeriya sun sanka, babu wanda zai zo kusa da ni, ba zan bari ba."

Kara karanta wannan

Ana gobe zaben Edo, Jonathan ya tura muhimmin sako ga INEC da jami'an tsaro

- Farfesa Rhoda Gumus

Farfesa Gumus ta ce akwai wani tsari ta ke bi wanda duk abin da ke faruwa cikin mintuna za ta sani domin gyarawa inda ta tabbatar cewa abin da take yi kenan tun bayan fara harkokin zaben jihar.

Yan sanda sun gargadi al'ummar Edo

Kun ji cewa al'ummar jihar Edo za su fito domin zaɓar gwamnan da zai jagorance su a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta buƙaci jama'a da su koma gidajensu bayan sun fito sun kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.