"Akwai Matsala": Gwamna Ya Gano Mugun Shirin da Ƴan Daba Ke Yi Ana Dab da Fara Zaɓe
- Gwamnatin jihar Edo ta ce wasu ƴan daba na shirin kai farmaki ofisoshin hukumar zaɓe INEC a dukkan ƙananan hukumomi 18
- Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a Chris Nehikhare ya faɗi yadda sojoji suka daƙile yunƙurin miyagun a yankin Oredo
- A yau Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024 al'ummar jihar Edo za su fita rumfunan zaɓe domin yanke wanda zai ci gaba da jagorantarsu na sheksru hudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Yayin da ya rage saura ƴan sa'o'i a fara kaɗa kuri'u, gwamnatin Edo karƙashin Gwamna Godwin Obaseki ta tono wata maƙarƙashiya.
Gwamnatin Obaseki ta ce ta gano cewa an ɗauko ƴan daba kuma suna nan suna shirin hargitsa ofisoshin hukumar zaɓe INEC a wasu kananan hukumomin Edo.
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Chris Nehikhare ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai a Benin, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Edo: Sojoji sun fatattaki ƴan daba
Nehikhare ya ce sojoji sun hana wasu miyagun siyasa mamaye ofishin INEC da ke karamar hukumar Oredo a babban birnin jihar.
A cewarsa, wannan ya sa gwamnatin Edo ke son jawo hankalin ƴan Najeriya da sauran ƙasashen duniya game da makircin da ƴan daban ke shiryawa na kwace ofisoshin INEC.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ana zargin wasu ƴan daban siyasa sun karɓe ofisoshin INEC na ƙananan hukumomin Estako ta Yamma da Esan ta Yamma.
Gwamnatin Edo ta gano makircin da aka shirya
Mista Nehikhare ya yi zargin cewa sune ƙulla wannan makircin ne domin karɓe iko da zaɓen gwamnan da za a yi da kuma magudi, rahoton Guardian.
"Sojoji ne suka fatattaki ƴan barandan siyasar kuma tun daga nan suka koma kan titunan da ke kusa da ofishin INEC, dakarun sojin sun hana su shiga wurin.
"Muna rokon dakarun sojoji su ɗauki makamancin wannan matakin a sauran kananan hukumomi 17," in ji shi.
Kwamishinan ya bayyana yankunan da suke tungar PDP da suka haɗa da Oredo, Egor, Ikpoba/Okha, kana ya yi kira ka mutanen Edo su fito su kaɗa kuri'unsu ba tare da tsoro ba.
Edo 2024: Yan sanda sun taƙaita zirga-zirga
A wani rahoton kuma rundunar yan sandan kasar nan ta umarci a takaita da zirga zirga a ranar zabe da zai gudana ranar Asabar a Edo.
Babban Sufeton yan sandan kasar nan, Kayode Egetokun ya bayar da umarnin a wani mataki na tabbatar da tsaro.
Asali: Legit.ng