“Barayi ba Su Kawo Gyara”: Obasanjo Ya Sake Dira kan Yan Siyasar Najeriya

“Barayi ba Su Kawo Gyara”: Obasanjo Ya Sake Dira kan Yan Siyasar Najeriya

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu yan siyasar Najeriya a matsayin barayi
  • Obasanjo ya ce babu yadda za a yi tsammnin shugabanci nagari daga yan siyasa da suke cin hanci a Najeriya
  • Tsohon shugaban ya ce ya kamata a yanzu dukan yan siyasa da ke cin hanci suna kulle a gidajen gyaran hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya sake caccakar yan siyasar Najeriya.

Obasanjo ya ce barayi ba za su taba tsinana komai a kan mulki ba wurin kawo abubuwan cigaba a kasa.

Obasanjo ya caccaki yan siyasa kan cin hanci
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya soki yan siyasar Najeriya kan cin hanci. Hoto: Phill Magakoe.
Asali: Getty Images

Cin hanci: Obasanjo ya soki yan siyasa

Kara karanta wannan

"Na san komai": Tinubu ya magantu game da halin kunci, ya fadi silar shan wahala

Tsohon shugaban Najeriya ya fadi haka ne a jihar Lagos a yau Juma'a 20 ga watan Satumbar 2024, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya ce shugabannin ko yan siyasa da suka kware a cin hanci babu wani abin kirki da za su kawo na cigaba.

Ya kwatanta yan siyasa da ke cin hanci da barayi inda ya ce ya kamata duk a daure su a gidajen gyaran hali, Daily Post ta ruwaito.

Obasanjo ya fadi halin yan siyasa

"Idan ka duba mutanen da suke cikin gwamnanti a yau kama daga bangaren zartarwa har dokoki ya kamata wasu daga cikinsu su kansace a gidan yari."
"Bai kamata ka yi tsammanin abin kirki daga barayi musamman wurin kawo cigaban kasa ba."

- Olusegun Obasanjo

Wannan na zuwa ne makwanni biyu bayan Obasanjo ya ce babu wata wahala a mulkin Najeriya kamar yadda ake tunani.

Kara karanta wannan

"Za mu ceto ku": Kwankwaso ya fadi niyyarsa game da mulki a 2027

Obasanjo ya ce ba kamar yadda ake zato ba Najeriya tana da sauki mulki kawai an rasa shugabanni ne da suka dace.

"Aiki ya kawo ni fadar shugaban kasa" - Tinubu

Mun baku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dalilin zuwansa fadar shugaban kasar Najeriya domin cire shakku.

Tinubu ya ce aiki ne ya kawo shi fadar shugaban kasa ba wai neman kudi da amfani da damar ta wani hanya ba.

Shugaban Najeriya ya kuma roki alumma hadin kai domin tabbatar da kawo sauyi a kasar Najeriya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.