"Za Mu Ceto Ku": Kwankwaso Ya Fadi Niyyarsa game da Mulki a 2027

"Za Mu Ceto Ku": Kwankwaso Ya Fadi Niyyarsa game da Mulki a 2027

  • Jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha alwashi kan zaben 2027 inda ya ce suna kan shiri
  • Kwankwaso ya ce yana da shirin tsamo yan Najeriya daga cikin kangin da suke ciki na mummunan yanayi da suka fada
  • Tsohon gwamnan Kano ya koka kan yadda yan kasar suka tsinci kansu a cikin wani irin yanayi na matsin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fadi niyyar da yake da ita game da mulkin Najeriya.

Kwankwaso ya ce babban abin da ya saka a gaba shi ne ceto Najeriya daga halin matsin tattalin arziki da take ciki.

Kwankwaso zai ceto yan Najeriya daga kangi
Rabiu Kwankwaso ya sha alwashin kwace mulki daga APC. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

2027: Rabiu Kwankwaso ya fadi shirin NNPP

Kara karanta wannan

Yunwa na neman kashe shi a Katsina, Kwankwaso ya ceci ran karamin yaro

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara ofishin NNPP a jihar Osun, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon jam'iyyar NNPP wanda ya samu wakilcin Dakta Rahila Mukhtar ya ce jam'iyyar ta shirya tsamo yan Najeriya a takaici, cewar rahoton Daily Post.

Kwankwaso ya ce jam'iyyarsa ta shirya inganta ayyukanta domin kwace mulki daga jam'iyyar APC duba da yadda ta ke gudanar da mulkinta.

Kwankwaso ya tona asirin yan siyasa

"Yan Najeriya yanzu sun gama fahimtar yadda yan siyasa ke talautar da su domin sake yaudararsu a zaben 2027."
"Ba zan taba yaudarsu ba sai dai in ceto kasar daga halin kunci da matsin tattalin arziki a Najeriya."
"NNPP tana da kyakkyawan tsari ga yan Najeriya, mun fara kiran jama'a tare da gyaran ofisoshinmu a jihohi inda muka samar musu da ababan hawa domin saukaka musu ayyuka."

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fadi yadda aka yi gumurzu wajen yunkurin kama Yahaya Bello

- Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya ceto yaro a Katsina

Kun ji cewa wani yaro mai shekaru 13, Abubakar Ibrahim ya samu lafiya bayan ya samu taimakon Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Abubakar Ibrahim, yaro ne 'dan asalin jihar Katsina ne da ke fama da cutar matsananciyar yunwa da ake kira tamowa.

An kawo yaron asibiti a Kano, kuma ya murmure an mayar da shi gaban iyayen shi a Katsina inda ya ke kara samun sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.