Gwamnonin PDP Sun Rabu Gida Biyu Kan Batun Sauke Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

Gwamnonin PDP Sun Rabu Gida Biyu Kan Batun Sauke Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

  • Gwamnonin PDP sun fara samun rabuwar kai kan shirin sauke muƙaddashin shugaban jam'iyya na ƙasa, Umar Damagum
  • Yayin da Gwamna Bala Mohammed ke jagorantar gwamnonin da ke son canza Damagum, wasu gwamnoni huɗu sun tsame kansu
  • Wata majiya daga kwamitin gudanarwa NWC ta ce gwamnoni bakwai na son a sauke Damagun, huɗu sun ce ya ci gaba da mulki, wasu biyu sun ce ba ruwansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ga dukkan alamu rikici ya ɓarke a tsakanin gwamnonin PDP kan batun muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum.

Ana ganin dai wannan babban matsala ce ga PDP a daidai lokacin da take ƙoƙarin warware duk wata rigima a cikin gida musamman rikicin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

PDP ta dare gida biyu, sabon shugaban jam'iyya ya karbi rantsuwar kama aiki a Arewa

Umar Damagum.
Batun canza shugaban PDP na kasa ya raba kawunan gwamnonin jam'iyyar Hoto: @OfficialPDP
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kiraye-kirayen a sauke shugaban PDP Umar Damagum, ya raba kawunan mambobin ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kawunan gwamnonin PDP suka rabu

Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce sun fara aiki da kwamitin gudanarwa NWC domin karɓe kujerar Damagum.

A ɗaya ɓangaren kuma Gwamna Seyi Makinde ya ce ba ya goyon bayan canza Umar Damagum daga shugabancin PDP.

Wani babba a kwamitin NWC na PDP ta ƙasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan Nyesom Wike, Damagum ya ƙara samun goyon bayan gwamnoni huɗu.

Ya bayyana gwamnonin hudu da Seyi Makinde na jihar Oyo, Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa, Caleb Mutfwang na jihar Filato da Agbu Kefas na jihar Taraba.

A cewar majiyar, gwamnonin jihohin Enugu da Zamfara, Peter Mbah da Dauda Lawal, sun tsaya a tsakiya ba su dauƙi kowane ɓangare ba, Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya tura tallafin miliyoyi ga mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri

Gwamnoni bakwai sun juyawa Damgum baya

Sai kuma gwamnoni bakwai ƙarƙashin jagorancin Bala Mohammed na jihar Bauchi waɗanda suka fara faɗi tashin sauke Umar Damagum daga shugabancin PDP.

Bayan Gwamna Bala, sauran gwamnoni shida da ke son a tsige Damagum sun haɗa da, gwamnan Osun, Ademola Adeleke, gwamnan Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri.

Sauran sune gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno.

Tun da aka naɗa shi shugaban riko, Damagum ya sha suka daga kusoshin PDP daban-daban, waɗanda ke ganin yana da hannu a rigingimun cikin gida.

PDP ta dare gida biyu a Katsina

A wani rahoton kuma abubuwan sun kara dagulewa a jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina bayan Yakubu Lado da Mustapha Inuwa sun raba gari.

Tsagin PDP karƙashin Sanata Yakubu Lado ya rantsar da sababbin shugabannin jam'iyya bayan kammala taruka a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262