Edo 2024: Ana Ta Hayaniya da Ɗan El Rufai Ya Goyi bayan 'Dan Takarar PDP
- An yi ta ce-ce-ku-ce bayan dan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya goyi bayan dan takarar PDP a zaben Edo
- Bashir El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ana daf da gudanar da zabe
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben sabon gwamnan Edo a gobe Asabar 21 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Yayin da ake shirin zaben jihar Edo, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fadi jam'iyyar da ya ke so.
Bashir El-Rufai ya nuna goyon bayansa ga dan takarar jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo a zaben gobe Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.
Edo: Dan El-Rufai ya bi bayan PDP
Dan tsohon gwamnan ya wallafa sunan Ighodalo da alamar tambarin zinari da ke nuna alamun nasara a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Asue Ighodalo, jihar Edo."
- Bashir El-Rufai
Bashir El-Rufai ya bar APC?
Bashir El-Rufai cikakken dan APC ne da ke goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu wanda mahaifinsa ya yi gwagwarmaya a zaben 2023.
Yaron tsohon gwamnan ya yi aiki a matsayin hadimin 'dan majalisar Kaduna a karkashin APC kuma ya goyi bayan Bola Tinubu a bara.
An caccaki Bashir El-Rufai kan zaben Edo
Nuna bangaren da Bashir ya jawo ka-ce-na-ce musamman a kafofin sadarwa duba da jam'iyyar da mahaifinsa, El-Rufai ya ke.
Sai dai wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da zargin rashin jituwa na El-Rufai da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Jama'a da dama suna ganin hakan cin dunduniyar jam'iyyar APC da kuma cin amana.
Edo: Jam'iyyu sun marawa APC baya
Kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyun siyasa tara sun rusa tsarinsu tare da marawa APC da dan takararta baya a zaben Edo mai zuwa.
Kasa da awanni 48 a zaben jihar, jam'iyyun sun ce za su yi aiki tukuru domin ganin dan takarar APC, Monday Okpebholo ya samu nasara.
Jam'iyyun NRM, SDP, ZLP, APM, ADP, APP, Accord, YPP da kuma AA ne suka marawa APC baya a wani taron manema labarai da suka kira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng