Zaɓen Gwamna 2024: Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Siyasar Edo

Zaɓen Gwamna 2024: Muhimman Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Siyasar Edo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Edo - Ranar Asabar 21 ga watan Satumba, 2024 hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamna a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Gwamna mai ci, Godwin Obaseki na PDP zai kammala wa'adinsa na biyu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada a ƙarshen wannan shekara 2024.

Ighodalo, Akpata da Monday Okpebholo.
Abjbuwan da za su ja hankali a zaben gwamnan Edo Hoto: @Aighodao, @m_akpakomiza, @OlamideAkpata
Asali: Twitter

Sisayar Edo na ɗaya daga cikin abubuwan da suke jan hankalin ƴan Najeriya musamman saboda yadda ake zaɓen gwamnan jihar daban da babban zaɓen gama gari.

Yayin da al'ummar Edo ke shirin fita su zaɓi wanda zai shugabance su na shekaru huɗu masu zuwa, Legit Hausa ta tattaro wasu muhimman abubuwan da ya dace ku sani.

Kara karanta wannan

Tsofaffin yan majalisa da wasu ƙusoshi sun koma a APC, PDP ta yi martani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Yanayin siyasar jihar Edo

Jihar mai arzikin man fetur da ke Kudu maso Kudu na daya daga cikin jahohin da ke da banbance-banbancen siyasa a Najeriya, Premium Times ta kawo.

Yayin da PDP ke mulki a jihar, APC na da biyu daga cikin sanatoci uku, Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa da Monday Okpebolo mai wakiltar Edo ta Tsakiya.

Sai kuma Labour Party da ta samu nasarar lashe zaɓen Edo ta Kudu, Bernards Neda shi ne ya zama sanata a zaɓen da ya gabata.

A ɗaya bangaren kuma ɗan majalisar wakilai ɗaya tal ne a PDP daga cikin ƴan majalisa tara da Edo ke da su, amma jam'iyya mai mulkin ita ke jan ragamar majalisar dokokin jiha.

2. Ƙarancin gogewar manyan ƴan takara 3

Zaben gwamnan jihar Edo na bana dai ya kunshi manyan ‘yan takara uku na sahun gaba da ke da karancin gogewar siyasa.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Babban hafsan tsaro ya yi gargadi yayin da ake shirin fara kada kuri'a

Wannan ne karo na farko da Asue Ighodalo na PDP da Akpata na LP Party suka shiga tseren neman takara a siyasa.

Sai kuma ɗan takarar APC, Monday Okpebholo, wanda ya samu nasarar zama sanata a zaɓen 2023, dukkansu dai suna da ƙarancin gogewa a siyasa.

3. Ƙabilanci da mulkin karɓa-karɓa

Edo ta Kudu ta yi mulki na tsawon shekaru 16 (Lucky Igbinedion, 1999-2007, da Obaseki, 2016-2024) yayin da Edo ta Arewa take da shekaru takwas (Oshiomhole, 2008-2016).

Edo ta Tsakiya ta yi takaitaccen lokaci ne a kan mulki bayan soke zaɓen gwamnan da ya fito daga yankin (Farfesa Oserheinem Osun, Mayu 29, 2007 - Nuwamba 12, 2008).

Ga dukkan alamu an samu matsaya mai karfi da za a magance wannan rashin daidaito domin ƴan takarar jam'iyyun PDP da APC sun fito ne daga Edo ta Tsakiya.

Dangane da batun kabilanci kuma ƙabilar Esans da ke da rinjaye a Edo ta Tsakiya, wasu tsiraru ne a jihar, kamar ’yan Okun da ke Jihar Kogi da ƙabilar Idomas a jihar Binuwai.

Kara karanta wannan

"In Sha Allahu za mu ɗinke ɓaraka," Gwamna ya gano waɗanda suka haddasa rikici a PDP

4. Edo da siyasar ubangida

Zaben gwamnan Edo da ke tafe ranar Asabar mai zuwa wata sabuwar fafatawa ce tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da tsohon gwamna Adams Oshiomhole.

Wannan dai shi ne karo na uku da za su kara tun 2020, duba da yadda ‘yan takarar jam'iyyunsu ba su da wata kwarewa a siyasance.

A zaɓen 2023, APC da Oshiomhole ke jagoranta ta lashe kujerun sanata biyu da ƴan majalisar wakilai shida, yayin da PDP da Obaseki suka samu kujerar ɗan majalisar wakilai ɗaya.

A zaben majalisar dokokin jihar Edo kuma, PDP ta lashe kujeru 15, APC ta samu 8 sai kuma LP da ta samu kujera ɗaya.

Ana ganin wannan ce dama ta ƙarshe da Oshiomhole zai nuna ƙarfin ikonsa kan Obaseki yayin da gwamnan ya samu damar da zai nuna karfinsa na siyasa.

5. Tinubu, Atiku da Obi sun nuna sha'awa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP sun nuna sha'awar jam'iyyunsu su karbi ragamar mulkin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Ana ta shiri: INEC, jam'iyyu da sauran al'amuran da ke wakana gabanin zaben Edo

Wannan zaɓe da ke tafe dai tamkar wata alamar nasara ce ga manyan ƴan takarar shugaban ƙasa uku a 2023, waɗanda ake kyautata zaton za su ƙara karawa a 2027.

PDP da Atiku na neman nasara ta kowane hali a zaɓen ranar Asabar domin ci gaba da mulkin Edo. Idan jihar ta subuce masu da yiwuwar su rasa ƙarfinsu a Kudu maso Kudu.

Jam’iyyar APC da Shugaba Tinubu na ƙoƙarin ƙwato mulkin jihar Edo, wanda suka sha kaye a 2020. Nasarar za ta sa adadin gwamnoninsu ya kai 21.

Edo 2024: Jerin ƴan takarar gwamna 17

Ku na da labarin hukumar zabe mai zaman kanta ta tantance adadin yan takarar da za su fafata a zaben Edo tare da mataimakansu a dukkan jam'iyyu

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku adadin dukkan yan takarar, mataimakansu da wasu bayanai da suka shafe su a zaben da za a gudanar gobe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262