Edo 2024: Gwamna Obaseki Ya Fadi Sharadin PDP Na Amincewa da Sakamakon Zabe

Edo 2024: Gwamna Obaseki Ya Fadi Sharadin PDP Na Amincewa da Sakamakon Zabe

  • Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana sharaɗin da zai sanya jam'iyyar PDP ta amince da sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ke tafe
  • Mai girma Obaseki ya bayyana cewa PDP za ta amince da sakamakon zaɓe wanda aka gudanar yadda ya kamata bisa gaskiya da adalci
  • Gwamnan mai shirin barin gado ya bayyana hakan ne ganawa da babban hafsan tsaro na ƙasa da sauran manyan jami'an soji a birnin Benin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana matsayar jam'iyyar PDP kan zaɓen gwamnan da ke tafe a karshen mako.

Gwamna Obaseki ya ce jam’iyyar PDP za ta amince da sakamakon zaɓe wanda aka gudanar yadda ya kamata bisa gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Gwamna ya faɗi tsohon gwamnan da yake zargi da alaƙa da ƴan bindiga

Gwamna Obaseki ya magantu kan zaben Edo
Gwamna Obaseki ya ce PDP za ta amince da sakamakon zaben gwamnan Edo Hoto: @GovernorObaseki
Asali: Twitter

Gwamnan Edo ya hadu da jami'an tsaro

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a Benin, babban birnin jihar Edo, yayin wata ganawa da babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, masu ruwa da tsaki da manyan jami'an sojoji gabanin zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ne a wani rubutu a shafinsa na X a dazu.

Gwamna Obaseki ya buƙaci jami’an tsaron da aka tura domin gudanar da zaɓen da su tabbatar an baiwa mutanen Edo damar zaɓar ƴan takarar da suke so.

Abin da PDP ta ke so a zaben Edo

"Ba wata alfarma muke nema ba amma muna bayyana cewa ya kamata a bar ƴan jihar Edo su samu ƴancin fitowa zaɓe domin zaɓar ƴan takarar da suke so. Za mu amince da sakamakon zaɓen da aka gudanar yadda ya kamata a bisa tsari."

Kara karanta wannan

"In Sha Allahu za mu ɗinke ɓaraka," Gwamna ya gano waɗanda suka haddasa rikici a PDP

"Tsawon shekaru takwas jami’an tsaro a jihar nan, sun ba mu haɗin kai wajen taimaka mana magance matsalolin tsaro."

- Gwamna Godwin Obaseki

Karanta wasu labaran kan zaɓen gwamnan Edo

Malami ya yi hasashe kan zaɓen gwamnan Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Prophet Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, Umuahia, jihar Abia, ya ce "dan takarar da aka raina" a zaɓen gwamnan jihar Edo na 2024 ne zai lashe zaɓen.

Da yake magana a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinsa na YouTube, Atuma ya yi hasashen cewa za a tafka shari'a bayan zaben jihar ta Edo.

Sai dai kuma malamin addinin ya bayyana cewa kotun sauraron kararrakin zaben ba za ta iya sauya sakamakon zaɓen ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng