PDP, APC, LP: Malami Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Lashe Zaben Gwamnan Edo

PDP, APC, LP: Malami Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Lashe Zaben Gwamnan Edo

  • Wani malamin addinin Kirista, Joel Atuma, ya bayyana hasashensa game da zaben gwamnan Edo da za a gudanar ranar Asabar
  • A cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, Atuma ya nuna cewa mutane za su yi mamakin wanda zai lashe zaben gwamnan jihar Edo
  • An ce ‘yan takara 17 ne za su fafata a zaben, amma ana ganin Olumide Akpata, Asue Ighodalo da Monday Okpebolo ne a sahun gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Prophet Joel Atuma na cocin The Lord Grace Provinces, Umuahia, jihar Abia, ya ce "dan takarar da aka raina" a zaben gwamnan jihar Edo na 2024 ne zai lashe zaben.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Jerin yan takara 17 da suke neman kujerar gwamna

Legit Hausa ta ruwaito cewa ranar Asabar, 21 ga Satumba aka shirya zaben Edo, inda Asue Ighodalo (PDP), Monday Okpebholo (APC), da Olumide Akpata (Labour Party) ne manyan 'yan takara.

Zaben gwamnan Edo: Malami ya hango dan takarar da zai lashe zabe
Malamin addini ya yi sabon hasashe gabanin zaben gwamnan Edo na 2024. Hoto: @m_akpakomiza/@HRH_Ujuaku/@OlumideAkpata
Asali: Twitter

Edo 2024: Hasashen sakamakon zaben gwamna

Da yake magana a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinsa na YouTube, Atuma ya yi hasashen cewa za a tafka shari'a bayan zaben jihar ta Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma malamin addinin ya bayyana cewa kotun sauraron kararrakin zaben ba za ta iya sauya sakamakon zaben ba.

A cewar malamin:

“A zaben gwamnan Edo, wanda ba a taba tsammani ba ne zai yi nasara. Za a je kotu, amma kotun ba za ta iya sauya sakamakon zaben ba.
“Ina gani kamar harafin E a sunan gwamnan jihar Edo na gaba. Ban ma san wanene mutumin ba; Ban san wanene dan takarar ba."

Kara karanta wannan

Olumide Akpata: Dan takarar LP mai barazana ga jam'iyyu a zaben Edo

Duba hasashen malamin addinin a nan kasa:

An dakatar da yakin neman zabe

A hannu daya, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su dakatar da duk wasu ayyukan yakin neman zabe a jihar Edo.

Hukumar a cikin wani sako da ta fitar a shafinta na X ta sake nanata cewa dole ne dukkanin jam'iyyu su kawo karshen yakin neman zabensu a yau Alhamis, 19 ga Satumba.

INEC ta kuma jaddada cewa haramun ne duk wata jam'iyyar siyasa a jihar Edo ta gudanar da gangami ko wani nau'in yakin neman zabe daga daren yau.

Edo: An fara jigilar kayan zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da fara jigilar muhimman kayayyakin zabe daga Abuja zuwa jihar Edo.

A cewar rundunar sojin, fara jigilar kayayyakin zaben zai ba hukumar INEC damar kammala shirye shirye da kuma gudanar da zaben Edo cikin nasara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.