PDP a Katsina Ta Dakatar da Tsohon Sanata daga Jam’iyyar? an Samu Karin Bayani

PDP a Katsina Ta Dakatar da Tsohon Sanata daga Jam’iyyar? an Samu Karin Bayani

  • Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta karyata labarin da ake yadawa cewa ta dakatar da Sanata Umar Ibrahim Tsauri
  • PDP a matsakin unguwa da ke Tsauri A ta ce wasu ne suka sanya hannun bogi a takardar dakatar da Sanata Tsauri
  • Sakataren jam'iyyar a yankin, Abdullahi Garba ya bayyana cewa wasu sun yi amfani da hakan domin bata sunan sanatan da PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Jam'iyyar PDP reshen unguwa a jihar Katsina ta yi magana kan jita-jitar dakatar da Sanata Umar Ibrahim Tsauri.

Shugabannin jam'iyyar a gundumar Tsauri A sun karyata labarin dakatar da sanatan Tsauri.

PDP ta magantu kan labarin dakatar da Sanata a Katsina
Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta musanta dakatar da Sanata Umar Ibrahim Tsauri. Hoto: Senator Umar Ibrahim Tsauri.
Asali: Facebook

Katsina: Ana zargin dakatar da Sanatn PDP

Kara karanta wannan

PDP ta gaji da lamarin gwamnan Sokoto, ta bukaci EFCC ta binciki N30bn da ya ware

Vanguard ta ruwaito cewa an samu wata wasika da ake zargin an saka hannun bogi domin dakatar da sanatan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar da ake zargin shugabanta da sakatare sun sanyawa hannu a ranar 13 ga watan Satumbar 2024 ta karade kafofin sadarwa, cewar rahoton Tribune.

Wata majiya ta ce an dakatar da sanatan ne saboda zargin yi wa jam'iyyar zagon-kasa da kalamai marasa kan gado ga shugabannin jam'iyyar PDP ta kasa.

Martanin PDP kan dakatar da Sanata Tsauri

Shugabannin jam'iyyar a Tsauri sun yi Allah wadai da kokarin bata suna sanatan da kuma PDP.

Suka ce kwamitin zartarwar jam'iyyar na kasa ke da ikon dakatar da Sanata mai babban mukami kamar Sanata Tsauri.

Sun zargi wadanda suka shirya hakan da cewa sun yi haka ne domin biyan bukatar kansu wurin yin amfani da shugabanta, Danjuma Abubakar.

Kara karanta wannan

Jiga jigan NNPP a jihohi 5 sun shiga matsala, an fara bincikensu

Sai dai sakataren jam'iyyar a unguwa, Abdullahi Garba ya ce matsalar ta fara ne tun bayan zaman sulhu da aka yi a karamar hukumar Kurfi.

Abdullahi ya ce an tsara zaman ne da Sanata Tsauri amma gama taron ke da aka samu wasikar dakatar da shi ta bogi tana yawo a kafofin sadarwa.

PDP ta soki ayyukan gwamnatin Sokoto

Kun ji cewa yayin da ake surutu kan gyaran bohula a jihar Sokoto, jam'iyyar PDP ta bukaci binciken Gwamna Ahmed Aliyu

Jam'iyyar ta yi Allah wadai da gwamnan ya sake ware makudan kudi har N30bn domin katange hanyoyi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.