"Tana Faranta Mani Rai," Gwamna Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Yake Ƙaunar Rawa

"Tana Faranta Mani Rai," Gwamna Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Yake Ƙaunar Rawa

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ce yana ƙaunar rawa ne saboda tana faranta masa rai amma sauke nauyin talakawa ya fi masa daɗi
  • Adeleke ya bayyana haka ne yayin da yake martani ga wani mutumi, wanda ya yaba da ƙoƙarin gwamnan da sukar da yake sha daga ƴan adawa
  • Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da gyaran asibitoci da gina hanyoyi a kowace ƙaramar hukuma a Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana dalilan da ya sa yake son rawa a rayuwarsa.

Gwamnan rawa kamar yadda wasu musamman ƴan adawa ke kiransa, ya ce yana ƙaunar rawa ba don komai ba sai don tana sa shi nishaɗi.

Kara karanta wannan

"In Sha Allahu za mu ɗinke ɓaraka," Gwamna ya gano waɗanda suka haddasa rikici a PDP

Gwamna Adeleke.
Gwamna Adeleke ya ce yana son rawa saboda tana faranta masa rai Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

Adeleke ya bayyana haka ne ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, 2024 yayin da yake martani ga wani ɗan jihar Osun a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko wani mai amfani da X, @Iwogoke, ya jinjinawa Gwamna Adeleke bisa yadda yake ƙoƙarin cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin kamfe.

Gwamna Adeleke ya sha yabo

Mutumin ya ce a lokacin da Gwamna Adeleke ya shagaltu da ƙoƙarin cika alkawarin kamfe a Osun, su kuma masu adawa da shi na ganin ba abin da ya iya sai rawa.

Iwogoke ya wallafa a shafinsa cewa:

"Ba wai ina zuzuta ka ba ne ranka ya daɗe, amma ƴan adawarka na tunanin rawa kawai ka iya.
"Yayin da suka koma suna surutu da kiranka gwamnan rawa kai kuma kana nan kana cika alkawarin da ka ɗaukar wa al'umma a lokacin kamfe."

Kara karanta wannan

Dattawan Zamfara sun ba Gwamna Dauda shawara kan Matawalle

Meyasa Gwamna Adekele yake son rawa?

Da yake ba shi amsa ta shafinsa na manhajar X, Gwamna Adeleke ya bayyana cewa yana son rawa ne saboda tana faranta masa rai.

"Rawa na ba ni farin ciki, amma cika alkawuran kamfen da na ɗauka da kuma shayar da mutane romon dimokuradiyya na faranta mun rai fiye da rawa."
"Muna ci gaba da aikin gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a akalla 200 daga cikin gundumomi 332, kuma ana ci gaba da aikin gina tituna a kowace karamar hukuma."

Gwamna Adeleke ya yiwa ma'aikata alƙawari

A wani labarin gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya yi alkawarin biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Gwamna Ademola Adeleke ta hannun kwamishinan yaɗa labaransa ya bayyana cewa walwalar ma'aikata na daga cikin abin da yake ba da fifiko a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262