Ana ta Shiri: INEC, Jam'iyyu da Sauran Al'amuran da ke Wakana gabanin Zaben Edo

Ana ta Shiri: INEC, Jam'iyyu da Sauran Al'amuran da ke Wakana gabanin Zaben Edo

Jihar Edo ta dauki harama yayin da ya rage kwana daya a gudanar da zaben gwamnan jihar, inda tuni hukumar zabe ta ke jan ragamar shirye shiryen zaben.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Shirin tunkarar zaben Edo wanda aka fuskanci zazzafan yakin neman zabe daga jam'iyyun APC, PDP, LP da sauransu ya kusa kammala.

Jami'an tsaro, hukumar INEC da jam'iyyun siyasa na ta shirin ganin an gudanar da zaben cikin nasara, yayin da kungiyoyin farar hula ke bayyana fargaba.

Jihar Edo
Ana shirin tunkarar zaben Edo a gobe Hoto: @NigAirFor
Asali: UGC

Legit ta tattaro wasu manyan abubuwan da ke faruwa yanzu haka a shirin zaben gwamna ranar Asabar a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shirin hukumar INEC a zaben Edo

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta rarraba muhimman kayan zabe ga kananan hukumomin jihar 18.

Hukumar ta kuma gargadi yan takara da magoya bayansu cewa an dakatar da neman kuri'a daga karfe 12:00 na ranar Juma'a, da karin gargadin ban da zuwa rumfunan zabe da tambarin jam'iyya.

2. Yan sanda, sojoji sun shiryawa zaben Edo

This day ta wallafa cewa rundunar sojan Najeriya ta ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a tabbata an yi zabe cikin kwanciyar hankali.

Babban hafsan tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa ya shaida wa gwamna Godwin Obaseki cewa za a yi aikin hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro a ranar 21 Satumba, 2024.

3. An bayar da hutu saboda zabe a Edo

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Majalisar amintattun PDP ta shiga ganawar gaggawa

Sahara reporters ta ruwaito cewa gwamna Godwin Obaseki ya ayyana Juma'a a matsayin ranar hutu domin ba jama'a damar kimtsa wa gabanin zaben Asabar.

An bayar da hutun domin jama'a, musamman ma'aikata su samu damar zuwa garuruwansu da za su kada kuri'a a zaben da ke tunkaro wa.

4. Zabe: Kungiya ta shiga fargaba a Edo

Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar Yiaga Africa na ganin akwai barazanar tashe-tashen hankula a zaben Edo da zai gudana ranar Asabar.

Dr. Aisha Abdullahi, shugabar Edo election mission ta kuma bayyana fargabar yadda jam'iyyu siyasa su ka ki sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jihar.

Edo 2024: Jam'iyyu 9 sun goyi bayan APC

A baya kun ji cewa jam'iyyar da ke mulki ta PDP a jihar Edo ta fara razana bayan an samu wasu jam'iyyu guda tara sun bayyana goyon baya ga APC a zaben gwamna mai zuwa.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Jerin yan takara 17 da suke neman kujerar gwamna

Cif Sam Arase, shugaban jam'iyyar NRM a jihar ne ya shaida wa manema labarai cewa NRM, SDP, ZLP, APM, ADP, APP, Accord, YPP da AA sun koma bayan APC a zaben.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.