Olumide Akpata: Dan Takarar LP Mai Barazana ga Jam'iyyu a Zaben Edo

Olumide Akpata: Dan Takarar LP Mai Barazana ga Jam'iyyu a Zaben Edo

  • A ranar Asabar,21 Satumba, 2024 ne hukumar zabe ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben sabon gwamna da za a rantsar a karshen shekara
  • Ana samun zazzafan yakin neman zabe tsakanin manyan jam'iyyun da ke tashe a jihar; APC, PDP mai mulki da LP
  • Olumide Akpata, dan jam'iyyar LP ne da ke barazana ga jam'iyyun biyu da za su gwabza a zaben da ya fara daukar dumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - A ranar Asabar mai zuwa ne mazauna jihar Edo za su nufi rumfunan zabe domin sake zabar gwamna bayan Godwin Obaseki ya cinye wa'adinsa.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Jerin yan takara 17 da suke neman kujerar gwamna

Jam'iyyar LP ta fitar da fitaccen lauya kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa, Olumide Akpata bayan doke takwarorinsa da kuri'a 316 a zaben fitar da gwani bayan tsunduma siyasa a 2023.

Olumide
Edo: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Olumide Akpata Hoto: Hoto: Olumide Akpata
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Barista Akpata ya bijiro da alkawura daban-daban da ya ke neman zabe da su a lokacin da yan kasar nan ke neman sauyi a dukkan matakai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Edo: Waye Olumide Akpbata?

An haifi Olumide Akpata a kasar Jamus a ranar 7 Oktoba, 1972, daga can su ka dawo Najeriya inda ya fara karatunsa a firamaren Nana da ke Warri.

Ya yi karatun sakandare a Federal Government College, amma ya karasa karatun a Kings' College da ke Legas, ya kammala karatun digirinsa a fannin shari'a a 1992.

Zaben Edo: Da me Akpata ke neman kuri'a?

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 kafin zabe, gwamnan Edo ya raba kyautar Naira biliyan 1 ga mata

BBC Pidgin ta wallafa cewa dan takarar LP a zaben Edo ya dauki manyan alkawura da jama'a ke neman gwamantocin kasar nan su yi masu.

Daga cikin abubuwan da ya kwadaitar da masu zabe shi ne zai tabbatar da zamanantar da harkar noma, cafke barayin gwamnati, farfado da harkar ilimi da farfado da tattalin arziki.

Kotu ta tabbatar da takarar Olumide Akpata

A baya mun kawo labarin cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar soke takarar Olumide Akpata da ke neman kujerar gwamna a zaben da zai gudanar ranar Asabar, 21 Satumba, 2024.

Alkalan kotun uku da su ka bayyana hukuncin da su ka zartar sun zargi mai shigar da kara, Kenneth Imasuangbon da take hanyoyin da jam'iyya ta bi na warware rikicin cikin gida kafin zuwa kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.