‘Jam’iyyar Yunwa:’ Atiku Ya Fadawa Mutanen Edo Abin da Zai Faru Idan PDP Ta Ci Zabe

‘Jam’iyyar Yunwa:’ Atiku Ya Fadawa Mutanen Edo Abin da Zai Faru Idan PDP Ta Ci Zabe

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira na musamman kan zaben gwamna da ake shirin yi a jihar Edo
  • Atiku Abubakar ya ce zaben APC a Edo zai kara mayar da jihar baya kuma hakan na nuni ne da cewa an zaɓi wahala a kan sauki
  • A ranar 21 ga watan Satumba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben gwamnoni a Edo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi kira ga al'ummar jihar Edo kan zaben dan takarar PDP.

Atiku Abubakar ya ce ya kamata mutanen jihar Edo su zabi Asue Ighodalo wanda ya tsaya takara a PDP domin kawo cigaba a jihar.

Kara karanta wannan

Daga 1991 zuwa 2024: Cikakken jerin gwamnonin soji da farar hula na jihar Edo

Atiku
Atiku ya yi gargadi kan zaben Edo. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Legit ta tattaro abin da Atiku Abubakar ya fada ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi kira a zabi PDP a Edo

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci al'ummar jihar Edo su zabi dan takarar PDP a zaben ranar Asabar mai zuwa.

Atiku ya ce ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo yana da nagarta kuma zai cire wa mutanen Edo kitse a wuta idan suka zabe shi a kan dan takarar APC.

Atiku ya ce APC jami'yyar yunwa ce

Punch ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya gargadi mutanen Edo a kan zaben APC inda ya ce jam'iyyar alama ce ta yunwa.

Ya kara da cewa APC ta jefa mutane cikin wahala amma shugabanninta suna fantamawa da dukiyar ƙasa.

APC ta kara kudin man fetur a Najeriya

Kara karanta wannan

Edo 2024: Abin da Shettima da Ganduje suka roki al'umma a kamfen zaben jihar

Atiku Abubakar ya ce jam'iyyar APC ta jefa Najeriya a matsala bayan kara kudin man fetur inda abubuwa suka lalace.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bayan yan Najeriya sun koka wajen yin zanga zanga aka rika kama su an ana kulle su.

An gama yakin neman zabe a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zaben Edo, an kawo karshen yakin neman zabe da aka yi na tsawon kwanaki.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaba APC, Abdullahi Ganduje sun samu halartar yakin neman zabe na karshe a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng