Zaben Edo: Gwamna Ya Gargadi Ma'aikata, Ya Fadi Babban Kuskuren da Za Su Yi
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya yi kira ga ma'aikatan gwamnatin jihar da su zaɓi jam'iyyar PDP a zaɓen gwamna da ke tafe
- Gwamna Obaseki ya yaba musu kan irin goyon bayan da suka ba shi a lokacin da ya kwashe yana gudanar da mulki a jihar Edo
- Obaseki ya ja kunnensu kan zaɓar APC inda ya ce su ne za su fara ji a jikinsu idan suka yi kuskuren kaɗa ƙuri'unsu ga jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya buƙaci ma’aikatan gwamnati da su zaɓi jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.
Gwamna Obaseki ya yi gargaɗin cewa idan jam’iyyar APC ta yi nasara, su ne farkon waɗanda za su fara ji a jikinsu.
Gwamna Obaseki ya godewa ma'aikata
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ne a wajen wani taro domin nuna godiyarsa ga ma'aikatan jihar gabanin zaɓen da ke tafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Obaseki ya bayyana jin daɗinsa da goyon bayan da suka ba shi a lokacin mulkinsa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Gwamnan ya kuma soki abokan hamayyarsa, yana mai cewa ba su san komai ba kuma ba su da ƙwarewa.
Wane gargaɗi gwamna ya yi wa ma'aikata?
"Na zo nan ne domin na yaba muku tare da yin godiya daga zuciyata. Ba tare da goyon bayanku ba, da ban cimma nasarorin da na samu ba."
"Wannan tafiya ce. Yayin da nake kammalawa, dole ne a ci gaba daga inda muka tsaya. Ba za mu yarda mu yi kuskure a ranar Asabar ba."
"Masu neman mulki ko ta halin ƙaƙa ba su da ilimi kuma ba su da ƙwarewa. Hatsarin barin irin waɗannan mutane su yi jagoranci yana da girma matuƙa."
"Duk wani kuskure da kuka yi, ku zai fara shafa kafin kowa."
- Godwin Obaseki
APC ta samu tagomashi a zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar Action Alliance (AA), Prince Tom Iseghohi-Okojie, ya janye daga shiga zaɓen.
Prince Tom Iseghohi-Okojie bayan janyewar, ya marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, baya a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng