Edo 2024: Muhimman Bayanai 5 game da Asue Ighodalo, Dan Takarar Gwamnan PDP

Edo 2024: Muhimman Bayanai 5 game da Asue Ighodalo, Dan Takarar Gwamnan PDP

  • Asue Ighodalo ya zama dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo a 2024 da za a gudanar ranar Asabar, 21 ga Satumbar 2024
  • Ighodalo ya kafa Banwo & Ighodalo, daya daga cikin manyan kamfanonin lauyoyi na Najeriya, kuma ana girmama shi a fannin shari'a
  • Baya ga sanin doka da kasuwanci, Ighodalo yana da taka rawa sosai a hidimar jama'a, ya fi karkata kan ilimi, kiwon lafiya, da tattali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Yayin da ta shirya tunkarar zaben gwamnan jihar Edo na 2024, jam’iyyar PDP ta tsayar da Asue Ighodalo a matsayin dan takararta.

Manyan ‘yan takara a zaben sun hada da Asue Ighodalo (PDP mai mulki), Olumide Akpata na Labour Party (LP) da Monday Okpebolo na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Jam'iyyar PDP ta kafa sharadi 1 na shiga yarjejeniyar zaman lafiya

Asue Ighodalo, dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo
Muhimman abubuwa a kan Asue Ighodalo, dan takarar PDP a zaben gwamnan Edo. Hoto: Asue Ighodalo
Asali: Facebook

Asue Ighodalo: Wanene 'dan takaran PDP a Edo?

Mun yi nazari ne kan tarihi da nasarorin Asue Ighodalo, fitaccen dan kasuwan Najeriya, masanin shari'a, kuma mai taimakon jama'a, kamar yadda BusinessDay ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fito daga tsatson da ke da zurfin ilimi da kwarewa a fannoni daban daban, tarbiyyar da Ighodalo ya samu ta tsara hanyar sana'arsa da cika burinsa.

Ga muhimman bayanai game da mutumin da ke fatan zai jagoranci jihar Edo:

Rayuwa da Ilimin Ighodalo

Ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziki a jami'ar Ibadan kafin ya yi digiri na biyu a fannin shari'a (LL.M) a makarantar koyon tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta Landan (LSE).

Shigowar Ighodalo a harkar kasuwanci ya fara ne daga fannin shari’a, inda ya yi aiki a matsayin lauya kuma ya samu gogewa sosai a Najeriya da Ingila.

Kara karanta wannan

Daga 1991 zuwa 2024: Cikakken jerin gwamnonin soji da farar hula na jihar Edo

Ayyukan Ighodalo a fannin shari'a

An rahoto cewa Ighodalo ya kafa Banwo & Ighodalo, daya daga cikin manyan kamfanonin lauyoyi na Najeriya.

Kamfanin ya ƙware a fannoni daban-daban, da suka hada da shari'ar kuɗin kamfanoni, manyan kasuwanni, makamashi da ayyukan more rayuwa.

Ana girmama Ighodalo sosai saboda gwanintarsa ​​a fannin shari'ar kasuwanci, hadakar kamfanoni da mallakarsu kuma ya ba da gudummawa sosai ga shari'ar Najeriya.

Kasuwanci da tsarin jagoranci

Baya ga aikinsa na shari'a, Asue Ighodalo ya shahara wajen inganta kyakkyawan tsarin tafiyar da harkokin kasuwanci da kuma kawo sauye-sauyen kasuwanci a Najeriya.

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa ya yi aiki a kwamitocin shuwagabannin manyan kamfanoni da suka hada da bankin Sterling da NESG, inda ya yi tasiri wajen sake fasalin tattalin arziki.

Ighodalo ya taka muhimmiyar rawa a kasuwannin hada-hadar kudi na Najeriya, an ce ya ba da shawarwari kan mu’amalolin da suka daidaita tattalin arzikin kasar.

Fannin hidima da taimakon jama'a

Kara karanta wannan

Ana rade radin tuge shi, Ganduje ya damƙi Sanata daga PDP zuwa APC

Asue Ighodalo ya na da dogon tarihin hidimtawa jama'a da ayyukan jin kai, galibi ya na mai da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, da ƙarfafa tattalin arziki.

Ya tsunduma cikin ayyukan jinkai daban-daban da ke inganta ilimi da sanin makamar aiki ga matasa marasa galihu a jihar Edo.

Ighodalo ya kuma kasance mai fafutukar neman sauye-sauyen manufofi a cikin ka'idojin kasuwanci, gudanar da mulki, da ci gaban tattalin arziki.

Abin da Ighodalo ya sanya a gaba

Ighodalo ya nunawa duniya abin da zai iya cimmawa ta hanyar cin buri, hazaka, da sadaukarwa ta gaske domin gina rayuwar al’umma da kasarsa.

Tare da kyakkyawan kuduri ga jihar Edo, Ighodalo ya ce zai mayar da hankali kan magance batutuwa kamar ci gaban tattalin arziki, ababen more rayuwa da sake fasalin ilimi.

Tunani, dabaru da kuma kwarewarsa a gudanar da harkokin kasuwanci da sanin shari'a su ne ginshinkansa na tunkarar dukkanin kalubalen jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Sani Danja ya sha kaye a neman takarar kujerar ciyaman karkashin NNPP

Edo: PDP ta kafa sabon sharadi

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP a Edo ta ce ba za ta shiga yarjejeniyar zaman lafiya ta jam'iyyun siyasar jihar ba har sai an biya dukkanin bukatunta.

A yayin da ya rage saura 'yan kwanaki a gudanar da zaben gwamnan Edo, PDP ta ce za ta shiga yarjejeniyar ne kawai idan aka sako mutanenta da aka tsare a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.