Badakalar N432bn: A Karon Farko, Uba Sani Ya Yi Magana kan Alakarsa da El Rufai

Badakalar N432bn: A Karon Farko, Uba Sani Ya Yi Magana kan Alakarsa da El Rufai

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya na yiwa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai bi-ta-da-kulli
  • Uba Sani ya ce tun 1999 ya ke da alaka mai kyau da dukkanin tsofaffin gwamnonin jihar kuma bai ware Malam Nasir El-Rufai ba
  • A cewar gwamnan, bai tsoma baki a harkokin majalisar jihar ba, wanda ke binciken zargin badalakar N432bn a gwamnatin El-Rufai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya fito ya shaidawa duniya alakar da ke tsakaninsa da magabacinsa, Malam Nasir El-Rufai.

Gwamna Uba Sani, ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa gwamnatinsa na yiwa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai bi-ta-da-kulli.

Kara karanta wannan

"Ka yi hakuri": Tsohon gwamna ya roki basarake gafara, ya yi nadamar aikinsa

Gwamna Uba Sani ya yi magana kan alakarsa da Nasir El-Rufai
Kaduna: Uba Sani ya musanta zargin da ake masa na yiwa magabacin sa, Nasir El-Rufai bi-ta-da-kulli. Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Alakar Uba Sani da Nasir El-Rufai

An ruwaito cewa gwamnan na Kaduna ya bayyana alakarsa da El-Rufai ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Talata 17 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya ce ya na da kyakkyawar alaka da dukkanin wadanda suka rike ragamar jihar Kaduna tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu.

Gwamnan ya bayyana tsohon El-Rufai da ke fuskantar tuhume-tuhume a matsayin abokinsa kuma dan uwansa.

Ya kara da cewa dukkanin gwamnonin da aka yi a Kaduna sun yi iya bakin kokarinsa wajen gudanar da mulkin jihar kuma ba zai ware kowa ba.

"El-Rufai ya yi kokari" - Uba Sani

Uba Sani ya tabbatar da cewa tsohon na Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi iya bakin kokarinsa wajen gudanar da al’amuran jihar.

Sai dai gwamnan ya jaddada cewa bai yi katsalandan a cikin harkokin majalisar dokokin jihar ba, wanda a halin yanzu ke binciken magabacinsa, El-Rufai.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

Gwamnan ya ce:

"Lokacin da suka ce majalisa ta zo da wannan bincike, ban yi shisshigi ba, gwamnatin jihar da ke karkashina ba ta yi ba, kawai na mayar da hankali ne kan aikina."

Kalli tattaunawa da gwamnan a nan kasa:

El-Rufai ya caccaki Uba Sani

A wani labarin, mun ruwaito cewa Malam Nasir El-Rufai ya caccaki gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani kan zargin satar kudi da ake yiwa tsohuwar gwamnatinsa.

Ta bakin tsofaffin kwamishinoninsa, El-Rufai ya ce zargin gwamnatinsa ta karkatar da kusan N423,115,028,072.88 ba gaskiya ba ne, makirci ne kawai aka shirya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.