Watanni 3 Kacal da Nada Su, Gwamna Ya Fatattaki Shugaban Ƙaramar Hukuma

Watanni 3 Kacal da Nada Su, Gwamna Ya Fatattaki Shugaban Ƙaramar Hukuma

  • Kasa da watanni uku bayan nada shugabannin ƙananan hukumomi, Gwamna Simi Fubara ya dakatar da daya daga cikinsu
  • Siminalayi Fubara ya sallami shugaban karamar hukumar Akuku-Toru, Otonye Briggs a yau Talata 17 ga watan Satumbar 2024
  • Gwamnan Ribas ya umarci Bitebobo Nelson Amieye ya karbi ragamar jagorancin karamar hukumar na wucin-gadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya dakatar da sabon shugaban karamar hukuma da ya nada watanni uku da suka wuce.

Gwamnan ya sallami shugaban karamar hukumar Akuku-Toru, Otonye Briggs daga mukaminsa a yau Talata 17 ga watan Satumbar 2024.

Gwamna ya kori shugaban karamar hukuma wata 3 bayan nada shi
Gwamna Siminalayi Fubara ya sallami shugaban karamar hukuma wata 3 da nada shi. Hoto: Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Rivers: Gwamna Fubara ya kori shugaban karamar hukuma

Kara karanta wannan

Awanni bayan dawowarsa daga China, Tinubu ya yi muhimmin nadi a ofishin Ribadu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Nelson Chukwudi ya fitar, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya ce sallamar Otonye Briggs zai fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan ya umarci Bitebobo Nelson Amieye ya karbi jagorancin karamar hukumar na wucin-gadi.

Har ila yau, Fubara ya umarci Otonye Briggs da ya mika dukkan abubuwan da ke hannunsa nan take.

Mene dalilin dakatar da ciyaman a Rivers?

Sai da har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a bayyana dalilin dakatar da shugaban karamar hukumar ba.

"An dakatar da shugaban karantar hukumar Akuku-Toru, Hon. Otonye Briggs daga mukaminsa nan take."
"Gwamnan ya umarci Hon. Bitebobo Nelson Amieye ya karbi jagorancin karamar hukumar a matsayin shugabanta."
“An umarci Barista Otonye Briggs ya tabbatar da mika dukan abubuwan da ke tare da shi mallakin karamar hukumar."

Kara karanta wannan

"Ka yi hakuri": Tsohon gwamna ya roki basarake gafara, ya yi nadamar aikinsa

- Cewar sanarwar

Wike ya sha alwashin nakasa Gwamna Fubara

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya caccaki Gwamna Siminalayi Fubara kan karairayi da yake yi masa.

Wike ya koka kan yadda ya sadaukar da wahalar da wasu suka sha domin tabbatar da Fubara ya zama gwamnan jihar.

Ministan ya ce har karshen rayuwarsa ba zai sake goyon bayan Fubara ba a siyasa saboda butulci da ya yi masa duk da sadaukarwa da aka yi masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.