Zaben Edo: Jam'iyyar PDP Ta Kafa Sharadi 1 na Shiga Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Zaben Edo: Jam'iyyar PDP Ta Kafa Sharadi 1 na Shiga Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Asue Ighodalo ya fadi wani muhimmin sharadi da gwamnatin tarayya da ‘yan sanda za su cika kafin PDP ta shiga yarjejeniyar zaman lafiya
  • Dan takarar gwamnan na Edo a PDP ya dage cewa dole ne gwamnati da ‘yan sanda su saki ‘yan jam'iyyar da ake tsare da su a birnin Abuja
  • Mista Ighodalo ya kuma dage kan cewa mutanen Edo ne kadai ke da ikon yanke hukunci kan wanda zai zama gwamnan jihar a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Edo na ranar 21 ga Satumba, 2024, Asue Ighodalo ya gindawa gwamnatin tarayya da 'yan sanda sharuda.

Kara karanta wannan

Daga 1991 zuwa 2024: Cikakken jerin gwamnonin soji da farar hula na jihar Edo

Mista Ighodalo ya ce jam'iyyar PDP a Edo ba za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba har sai gwamnati da 'yan sanda sun cika dukkanin sharuddansu.

Asue Ighodalo ya yi magana akan yarjejeniyar zaman lafiya, kwanaki kadan kafin zaben Edo.
Jam'iyyar PDP ta kafawa gwamnatin tarayya da 'yan sanda sharadi kafin shiga yarjejeniya a Edo. Hoto: @Aighodalo
Asali: Twitter

Ighodalo, wanda ya yi magana da Channels TV a Litinin, ya koka kan yadda aka kama wasu ‘yan PDP tare da tsare su ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharadin PDP na shiga yarjejeniya a Edo

Dan takarar ya bayyana cewa jam'iyyarsa za ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ne kadai idan aka sako magoya bayansa da ke tsare a hannun ‘yan sanda a Abuja.

Jaridar The Punch ta rahoto Ighodalo na cewa:

“Muna da sharuɗɗa da dama, yawancin sharuɗɗan yanzu an cika su amma saura ɗaya ne ya rage. Yawancin mutanenmu an kama su bisa zalunci.

Kara karanta wannan

Kitimurmurar Atiku da Wike: Shugaban jam'iyya ya fede biri har wutsiya game da zunuban Wike a PDP

Domin haka, ko dai su kai dukkanin mutanenmu kotu ko kuma a bayar da belinsu. Idan aka cimma wannan sharadi za mu rattaba hannu kan yarjejeniyar."

"A mutu ko a yi rai" - Gwamnan Edo, Obaseki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Edo Godwin Obaseki, ya bayyana zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a matsayin “ko a mutu ko a yi rai".

An ce Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ne a taron yakin neman zaben PDP a Ekenwan da ke cikin Benin babban birnin jihar Edo inda ya caccaki Adams Oshiomhole.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.