Rigimar PDP: Gwamna a Arewa Ya Mayar da Zazzafan Martani ga Ministan Tinubu

Rigimar PDP: Gwamna a Arewa Ya Mayar da Zazzafan Martani ga Ministan Tinubu

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya mayar da martani ga ministan Abuja kan barazanar da ya yi wa gwamnonin PDP
  • Sanata Bala ya ce ba wanda zai kunna wuta a Bauchi ya ci nasara saboda akwai wadataccen ruwan da ba zai bar wutar ta ci ba
  • Gwamnan Bauchi ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar kwamitin gudanarwa NWC na jam'iyyar PDP ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Gwamna Bala Muhammed ya ce babu wanda zai kunna wuta a jihar Bauchi kuma ya ci galaba saboda akwai isasshen ruwan kashe wutar.

Ya faɗi haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin gudanarwa (NWC) na jam’iyyar PDP ta ƙasa ranar Talata a fadar gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

"Kin koyi rayuwa": Gwamna ya fadi yadda aka zalunci ƴarsa a sansanin NYSC

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan Bauchi ya maida martani ga Wike, ya ce babu wanda zai iya kunna wuta a jiharsa Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Facebook

Gwamna Bala ya mayar da martani ga Wike

Daily Trust ta ce wannan shi ne karon farko da gwamnan ya mayar da martani ga barazanar da ministan Abuja, Nyesom Wike ya yiwa gwamnonin PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ruwayar Channels tv, Bala Mohammed ya ce:

"Kanmu a haɗe yake, babu wanda zai iya kunna mana wuta a Bauchi, muna da isasshen ruwan da za mu kashe wutar, shi kansa abokina da ya faɗi haka ba laifinsa ba ne.
"Watakila na fadi wani abu ne da ya bata masa rai amma ba wani saɓani tsakaninmu. Abokantaka daban, aiki daban, shugabancin al'umma shi ma gurbinsa daban.

Rikicin Wike da gwamnonin PDP

Idan ba ku manta ba Wike ya soki gwamnonin PDP bisa tsoma baki a harkokin siyasar Ribas, inda ya yi barazanar cewa zai kunno masu wuta a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Ana murnar kisan ubangidan Bello Turji, gwamna ya ƙara tona badaƙalar ministan Tinubu

A wani taro da suka yi a tsakiyar watan Agusta, gwamnonin PDP sun ayyana Simi Fubara, wanda ke takun saƙa da Wike, a matsayin jagoran jam'iyya a Ribas.

Gwamna Bala ya yaba da ziyarar NWC

Da yake jawabi yau Talata, Gwamna Bala ya ce wannan ziyara da kwamitin NWC na ƙasa ya kai masa ya kara nuna cewa har yanzun Najeriya na fatan samun sauyi.

"Babu jam'iyyar da ta tsira daga rikicin cikin gida, dole a samu saɓani nan da can, abin da ya kamata shi ne mu girmama juna, mu jingine burikanmu a gefe, mu mutunta juna."
"Duk wasu ayyukan ci gaba a kasar nan PDP ce ta yi shiyasa tun da ta bar mulki babu wani abin a zo a gani da aka ƙara yi"

- Gwamna Bala Mohammed

Shugaban PDP ya yi magana kan zunuban Wike

A wani rahoton kuma shugaban PDP ya yi tsokaci kan lamarin Nyesom Wike da korafe-korafen da ake yi a kansa bayan zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a Bauchi: Gwamnati ta bukaci ‘yan sanda su tuhumi sanatan APC

Tun bayan rasa takarar shugaban kasa a zaɓen fitar da gwanin PDP, Wike ya fara rabar APC har ta kai ya zama minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262