“Ku Daina Neman Taimakon Ubangiji”: Tsohon Minista Ya Shawarci Yan Siyasa
- Tsohon Ministan shari'a a mulkin shugaba Olusegun Obasanjo ya shawarci yan siyasa kan magudin zabe a Najeriya
- Kanu Agabi ya ce babu yadda za a yi tun daga zabukan tsaida gwani a yi magudi kuma a yi tsammani taimakon Ubangiji
- Lauyan ya koka kan yadda shugabannin yanzu suka koma bautar neman gidaje da kudi da kuma mata a rayuwarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan Shari'a, Kanu Agabi SAN ya shawarci yan siyasa masu neman mukamai game da zabe.
Agabi ya shawarci yan siyasar da su tabbatar sun yi gaskiya a duk abubuwan da za su yi domin wanke kansu.
Tsohon Minista ya gargadi yan siyasa kan magudi
Tsohon Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Litinin 16 ga watan Satumbar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce babu yadda za a yi mutum ya ci amana da magudin zaben sannan ya yi tsammani Ubangiji yana tare da shi, cewar rahoton Daily Trust.
Agabi ya ce abin takaici ne yadda ake magudi tun daga zabukan fitar da gwani har zuwa manyan zabukan da ake yi.
Kanu Agabi ya koka da halin yan siyasa
"Ana magudin zabe tun daga matakin tsaida gwanin jam'iyya, ofis din da ka samu ta hanyar sata kake son Ubangiji ya kasance tare da kai"?
"Za ka iya yin addu'a kan ofishin ko kuma yin wani abin kirki? Wannan shi ne babbar matsalar."
"Mun baro mulkin mallaka amma shugabanninmu suna kokarin mayar da mu baya kan soyayyar kudi da mata da gidaje."
- Kanu Agabi
'Dan takarar gwamna ya marawa APC baya
Kun ji cewa dan takarar gwamnan Edo a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar AA ya haƙura da takara a zaɓen na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.
Prince Tom Iseghohi-Okojie ya marawa ɗan takarar jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo baya a zaɓen gwamnan da ke tafe.
Ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa Sanata Okpebholo zai kawo shugabanci na gari a jihar ya samu nasarar zama gwamna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng