Zaben Edo: Muhimman Abubuwan Sani 7 Dangane da Dan Takarar APC, Okpebholo

Zaben Edo: Muhimman Abubuwan Sani 7 Dangane da Dan Takarar APC, Okpebholo

  • Monday Okpebholo shi ne ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Edo da ke tafe a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
  • Bayan zama babban ɗan siyasa a jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo mabiyin addinin Kirista ne kuma shahararren ɗan kasuwa
  • Kwanaki kaɗan kafin zuwan zaɓen, mun tattaro muku muhimman abubuwa dangane da ɗan takarar da ke son ya gaji Gwamna Godwin Obaseki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Sanata Monday Okpebholo ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Edo a ƙarƙashin jam'iyyar APC bayan ya yi nasara a zaɓen fidda gwanin da jam'iyyar ta gudanar.

Bayan zama ɗan takara a zaɓen, akwai abubuwa da dama da ƴan Najeriya musamman al'ummar jihar Edo ba su sani ba dangane da Sanata Monday Okpebholo.

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

Dan takarar APC a zaben Edo Sanata Monday Okpebholo
Sanata Monday Okpebholo na daga cikin 'yan takarar zaben gwamnan Edo Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Abubuwan sani kan Monday Okpebholo na APC

Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dangane da ɗan takarar na APC wanda yake son ya gaji Gwamna Godwin Obaseki wajen mulkin jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Shekarun Monday Okpebholo

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito an haifi Monday Okpebholo ne a shekarar 1970 a garin Uromi na jihar Edo. Yana da shekara 53 a duniya.

2. Karatunsa

Monday Okpebholo ya fara karatunsa ne a Uromi. Bayan ya kammala firamare da sakandire ya wuce jami'ar Benin (UNIBEN).

A jami'ar UNIBEN ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziƙin noma da digirin digirgir a fannin ilmin gudanar da shugabancin jama'a.

Ya kuma yi digirin digirgir a fannin ilimin tattalin arzikin gona a jami'ar Ibadan (UI).

3. Iyalan Monday Okpebholo

Sanata Monday Okpebholo yana da mata sannan Allah ya albarkaci aurensu da ƴaƴa huɗu.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Dan takarar gwamna ya janye, ya marawa APC baya

4. Monday Okpebholo ɗan kasuwa ne

Sanata Monday Okpebholo ɗan kasuwa ne wanda ya shahara a fannoni da dama na kasuwanci.

Okpebholo yana harkokin kasuwanci da suka haɗa da fannin gine-gine, fetur da iskar gas da noma.

5. Tsohon jigo ne a PDP

Sanata Monday Okpebholo ya fara siyasa ne a shekarar 2003 lokacin da ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

6. Okpebholo mamba ne a cocin RCCG

Bayan kasancewarsa ɗan siyasa, Sanata Monday Okpebholo mabiyin addinin Kirista ne kuma mamba a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG).

7. Okpebholo tsohon Sanata ne

Sanata Monday Okpebholo ya wakilci mazaɓar Edo ta Tsakiya a majalisar dattawa ta 10.

A watan Fabrairun 2024, ya lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC.

Ɗan takara ya janye a zaɓen Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jihar Edo na jam'iyyar Action Alliance (AA), Prince Tom Iseghohi-Okojie, ya janye daga yin takara a zaɓen.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Kalamam gwamnan PDP sun tayar da kura ana dab da fara zabe

Prince Tom Iseghohi-Okojie bayan janyewa daga takarar ya marawa ɗan jam'iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, baya a zaɓen wanda za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng