Edo 2024: Abin da Shettima da Ganduje Suka Roki Al'umma a Kamfen Zaben Jihar

Edo 2024: Abin da Shettima da Ganduje Suka Roki Al'umma a Kamfen Zaben Jihar

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben Edo, an kawo karshen kamfen da aka yi na tsawon kwanaki a jihar
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaba APC, Abdullahi Ganduje sun samu halartar kamfen
  • An gudanar da kamfen ne a jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 a Benin City inda Shettima ya roki al'umma su zabi APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - A jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 aka gudanar da kamfen karshe a jihar Edo.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban APC, Abdullahi Ganduje sun samu halarta.

Shettima da Ganduje sun yi jawabi a kamfen karshe na zaben jihar Edo
Kashim Shettima da Abdullahi Ganduje sun shawarci al'umma kan zaben jihar Edo. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Shettima ya sun roki al'umma zabar APC

Kara karanta wannan

"Ka yi hakuri": Tsohon gwamna ya roki basarake gafara, ya yi nadamar aikinsa

Hadimin Shettima, Stanley Nkwocha shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Kashim ya ba yan jihar Edo shawara kan muhimmancin zaben dan takarar APC a ranar Asabar mai zuwa.

Kashim ya ce jihar Edo na bukatar mutum mai tunani kuma wanda jama'a suke so domin ciyar da jihar gaba.

"Ko kai Musulmi ne ko Kirista, tsoho ko yaro, mace ko namiji, ko daga kabilar Esan ko Afemai duka bukatarmu mu samu cigaba ne "

- Kashim Shettima

Ganduje ya tallata APC ga yan Edo

A bangarensa, shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce yan jihar sun sha wahala na tsawon shekaru takwas.

Ganduje ya ce ya kamata yanzu su zabi APC domin cire su a kangin da suka fada na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Ana rade radin tuge shi, Ganduje ya damƙi Sanata daga PDP zuwa APC

Sauran wadanda suka halarci kamfen sun hada da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Adams Oshiomhole.

Sai kuma dan takarar gwamna a APC, Monday Okpebholo da sauran jita-jigan jam'iyyar da dama.

Sanata ya koma APC ana shirin zabe

Kun ji cewa Jam'iyyar APC ta sake yin babban kamu bayan tsohon sanata ya sauya sheka daga PDP a jihar Edo ana shirin yin zaɓe.

Sanata Francis Alimikhena wanda ya wakilci Edo ta Arewa ya watsar da PDP ne a jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.