Zaben Edo: Kalaman Gwamnan PDP Sun Tayar da Kura ana Dab da Fara Zabe

Zaben Edo: Kalaman Gwamnan PDP Sun Tayar da Kura ana Dab da Fara Zabe

  • Gwamnan jihar Edo ya yi kalamai masu kaushi yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar da ke tafe
  • Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa zaɓen wanda ke tafe a mutu ko a yi rai ne
  • Kalaman na Gwamna Obaseki na zuwa ne yayin da ya rage saura ƴan kwanaki kaɗan al'ummar jihar su fito domin kaɗa ƙuri'unsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a matsayin “ko a mutu ko a yi rai".

A ranar 21 ga watan Satumba ne ake sa ran za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Edo.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Shugaban PDP ya sha sabon alwashi, ya gargadi INEC

Obaseki ya magantu kan zaben Edo
Gwamna Obaseki ya ce zaben Edo a mutu ko a yi rai ne Hoto: @Governor Obaseki
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ne a wajen yaƙin neman zaɓen PDP a yankin Ekenwan da ke cikin birnin Benin babban birnin jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Obaseki ya ce kan zaɓen Edo?

Gwamna Obaseki ya caccaki magabacinsa Adams Oshiomhole, kan rashin yin kataɓus a lokacin mulkinsa, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

"Wanda na karɓi ragamar mulki a hannunsa ba ya mutunta mutanenmu, ba ya girmama mata, ya ƙarfafa karuwanci da safarar mata."
"Lokacin da na karɓi mulki, ƴan fanshonmu suna sanya baƙaƙen kaya a ranar ma’aikata, amma a yau suna sanya farare."
"Lokacin da na hau mulki, matasanmu ba su da aikin yi, amma shin yau ba su da aikin yi? Bayan shekara takwas, shin Edo ba ta daga cikin jihohin da suka fi tsaro?"
"Wannan zaɓen a mutu ko a yi rai ne. Kuna son rashin tsaro? Kuna son mutanen da ba su je makaranta su jagorance mu ba? Asabar mai zuwa ne zaɓe, za ku zaɓi PDP, gwamnan mu na gaba shi ne Asue Ighodalo."

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

- Gwamna Godwin Obaseki

Shugaban PDP ya magantu kan zaɓen Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Illiya Damagum, ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo

Umar Damagum ya bayyana cewa ƴaƴan jam’iyyar za su yi amfani da jininsu wajen kare ƙuri’unsu a zaɓen gwamnan da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng