Zaben Edo: Shugaban PDP Ya Sha Sabon Alwashi, Ya Gargadi INEC

Zaben Edo: Shugaban PDP Ya Sha Sabon Alwashi, Ya Gargadi INEC

  • Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya ja kunnen hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) kan zaɓen gwamnan jihar Edo
  • Umar Damagum ya gargaɗi INEC kan yin maguɗin zaɓe ta hanyar sanar da sakamakon zaɓen cikin tsakar dare
  • Ya bayyana cewa ƴaƴan jam'iyyar PDP za su fito su kare ƙuri'unsu da jininsu domin tabbatar da cewa ba a yi musu maguɗi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Illiya Damagum, ya yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo.

Umar Damagum ya bayyana cewa ƴaƴan jam’iyyar za su yi amfani da jininsu wajen kare ƙuri’unsu a zaɓen gwamnan da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Gwamna Obaseki ya fallasa makarkashiyar da ake yiwa PDP

Damagum ya gargadi INEC
Umar Damagum ya ce PDP za ta kare kuri'unta a zaben gwamnan Edo Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Shugaban na PDP ya kuma gargaɗi hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) kan sanar da sakamakon zaɓen cikin tsakar dare, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Me shugaban PDP ya ce kan zaɓen Edo?

Damagum ya bayyana haka ne a lokacin babban taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar PDP a Edo, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya kuma miƙa tutar jam’iyyar ga ɗan takarar gwamna, Dr Asue Ighodalo.

"Zuwa ga INEC, ba mu son sanar da sakamakon zaɓe cikin tsakar dare. Za mu yi taka tsantsan kuma mu tabbatar da cewa hakan bai faru ba."
"Kuma, mun san za su yi maguɗin zaɓe, wannan ba barazana ba ce, amma da gaske muke kuma za mu kare ƙuri’unmu da jininmu da komai."
"Ga mutanen ƙasar nan, ku sa ido kan zaɓen Edo, zai zama abin gwaji ga dimokuraɗiyyar mu. Idan suka yi abin da bai dace ba, yana nufin suna neman rashin zaman lafiya. Mun san za su yi yunƙurin yin hakan, amma za mu bijire musu.”

Kara karanta wannan

Kin shiga zanga zanga ya yi riba, gwamna ya ba matasa kyautar N310m

- Umar Iliya Damagum

Sai dai ya yi kira ga jam’iyyar da magoya bayanta da su fito ƙwan su da ƙwarƙwatarsu su zaɓi PDP tare da kare ƙuri’unsu.

Tsohon ɗan majalisar APC ya koma PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo na jam'iyyar APC ya sauya sheƙa zuwa PDP mai mulki a jihar.

Honarabul Emmanuel Agbaje ya koma jam'iyyar PDP ne kwanaki kaɗan bayan ya fice daga jam'iyyar APC ana sauran ƴan kwanaki a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng