“Ka Yi Hakuri”: Tsohon Gwamna Ya Roki Basarake Gafara, Ya Yi Nadamar Aikinsa

“Ka Yi Hakuri”: Tsohon Gwamna Ya Roki Basarake Gafara, Ya Yi Nadamar Aikinsa

  • Tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya roki basarake a jihar Edo kan kura-kurai da ya tafka lokacin yana gwamna
  • Oshiomhole ya nemi afuwar Esama na birnin Benin, Gabriel Igbinedion inda yace ya dauki basaraken a matsayin uba a gare shi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Sanata Adams Oshiomhole ya nemi afuwar basarake a jihar Edo kan abubuwan da suka faru a baya.

Oshimhole wanda ke wakiltar Edo ta Arewa ya mulki jihar a matsayin gwamna har na tsawon wa'adi biyu.

Sanatan APC ya nemi afuwar fitaccen basarake
Sanata Adams Oshiomhole ya nemi afuwar Esama na Benin kan kura-kurai da ya yi a baya. Hoto: Adams Oshiomhole.
Asali: Facebook

Edo: Oshiomhole ya roki afuwa daga basarake

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

Sanatan ya fadi haka ne a jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 yayin taya basaraken murnar cika shekaru 90, cewar rahoton Vanguard.

Oshimhole ya nemi afuwar Esama na Benin, Gabriel Igbinedion kan kura-kurai da ya yi masa lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Tsohon gwamnan ya kwatanta Igbinedion a matsayin uba tare da yaba masa kan irin gudunmawa da ya kawowa al'umma, Punch ta ruwaito.

Oshiomhole ya fadi gudunmawar basaraken ga al'umma

"Ka hada kan mutanen yankunan Arewa da Kudu da Gabas da kuma Yamma daga addinai daban-daban da kuma siyasa."
"Ina son yin amfani da wannan dama wurin tuna goyon baya da ka bani a 2007 da 2008 saboda ba dan haka ba, da ba zan zama gwamnan jihar Edo ba."
"Ina so na fadi gaskiya, watakila na yi wasu abubuwa da ba su kamata ba lokacin ina gwamna, ina neman yafiya daga gare ka."

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Admas Oshimhole

Obaseki ya fadi silar fadarsa da Oshiomhole

Kun ji cewa yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya fadi ainihin abin da ya haɗa shi da Adams Oshiomhole.

Obaseki ya ce kawai domin ya shirya jana'iza ta musamman ga jigon PDP, Cif Tony Anenih shi ne ya batawa Oshiomhole rai.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kamfen zaben gwamnan jihar da za a yi a watan Satumbar 2024 da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.