Ana Rade Radin Tuge Shi, Ganduje Ya Damƙi Sanata daga PDP Zuwa APC
- Jam'iyyar APC ta sake yin babban kamu bayan tsohon sanata ya sauya sheka daga PDP a jihar Edo ana shirin yin zaɓe
- Sanata Francis Alimikhena wanda ya wakilci Edo ta Arewa ya watsar da PDP ne a yau Asabar 14 ga watan Satumbar 2024
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar Asabar 21 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jam'iyyar PDP ta yi babban rashi.
Tsohon sanatan Edo ta Arewa, Francis Alimikhena ya fice daga jam'iyyar mai mulkin jihar zuwa APC.
Edo: Tsohon Sanatan PDP ya dawo APC
Jigon APC a karamar hukumar Etsako ta Yamma, Zibiri Muhammed shi ya tabbatar da haka ga jaridar Punch.
Muhammad ya ce tsohon sanatan yanzu haka yana shirin dawowa da jiga-jigan PDP zuwa jam'iyya mai mulkin Najeriya.
Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje shi zai karbi sanatan a ranar kamfen karshe a jihar.
"Tabbas Sanata Alimikhena ya zama ɗan APC, ya koma jam'iyyar a hukumance a yau Asabar."
"Shugaban APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje shi zai karbi sanatan a ranar karshe na kamfen zaben gwamnan jihar."
- Zibiri Muhammed
Yadda sanata ya gwabza da Adams Oshiomhole
Sanata Alimikhena ya wakilci Edo ta Arewa har sau biyu a Majalisar Dattawa ƙarƙashin APC, Daily Post ta ruwaito.
Sanatan ya watsar da APC zuwa PDP bayan rasa tikiti ga Sanata Adams Oshiomhole a zaben 2023.
Bayan komawarsa PDP, sanatan ya tsaya takara, ya gwabza a zabe da Oshiomhole inda ya yi rashin nasara.
PDP ta ki sanya hannu a yarjejeniya
Kun ji cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi fatali da bukatar tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar kan zabe.
Abdulsalami ya bukaci gwamnan ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin zaben gwamnan da za a yi a Edo.
Sai dai gwamnan ya ce ba zai sanya hannu a yarjejeniyar ba saboda babu alamun zaman lafiya bayan cafke 'yan PDP 60.
Asali: Legit.ng