Dan Takarar Shugaban Kasa na Neman Muƙamin Mataimaki a 2027? Ya Yi Magana

Dan Takarar Shugaban Kasa na Neman Muƙamin Mataimaki a 2027? Ya Yi Magana

  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa yana neman a ba shi mataimakin shugaban kasa a 2027
  • Obi ya ce wannan labari da ake yadawa babu kamshin gaskiya a ciki ko kadan ba shi da niyyar barin jam'iyyar LP
  • Dan takarar shugaban kasa a LP ya ce ba a matse yake ta kowane hali sai ya samu shugabancin Najeriya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya yi magana kan neman mataimaki a zaben 2027.

Peter Obi ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa yana son muƙamin mataimakin shugaban kasa inda ya ce babu kamshin gaskiya a labarin da ake yadawa.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban APC ya yi hasashen makomar Shugaba Tinubu a 2027

Peter Obi ya ƙaryata jita jitar neman kujerar matakin shugaban kasa a 2027
Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya musanta neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2027. Hoto: Peter Obi.
Asali: Facebook

2027: Obi ya yi magana kan zabe

Obi ya yi martanin ne a yau Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 a shafinsa na X inda ya yi fatali da rade-radin.

Dan takarar ya ce ba shi da niyyar kasancewa shugaban kasa ko mataimaki da sauran mukamai ta kowane hali.

Ya ce idan har haɗaka wasu ke so to za su iya bayyana muradunsu domin ya duba ko tafiyarsu za ta yi.

Har ila yau, Obi ya tabbatar da cewa yana nan a LP kuma babu abin da zai fitar da shi a cikinta.

Musabbabin martanin da Peter Obi ya yi

Tsohon gwamnan Anambra ya yi martanin ne bayan rade-radin cewa yana neman a ba shi mukamin mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace Bello Yabo? Shehi ya yi maganar 'garkuwa' da shi da 'kamen' DSS

Martanin ya biyo bayan wata hira da ya yi da yan jaridu kan zaben 2027 inda ya ce an juya maganar saboda siyasa.

LP ta magantu kan tikitin Peter Obi

Kun ji cewa da alama rikicin jam'iyyar Labour zai sake daukar sabon salo yayin da wani tsagin jam'iyyar ya ce ba zai ajiyewa Peter Obi tikitin takara ba.

Tsagin jam'iyyar karkashin Julius Abure ya ce zai ba dukkanin 'yan Najeriya da suka cancanta damar neman tikitin takara a zaben 2027.

Matakin da Abure ya dauka ya sabawa matakin da aka cimmawa a babban taron jam'iyyar wanda ya ayyana Obi a matsayin dan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.