APC, NNPP, LP ba Jam’iyyu ba ne, Shugaban PDP Ya Tona Manufar Kwankwaso da Obi

APC, NNPP, LP ba Jam’iyyu ba ne, Shugaban PDP Ya Tona Manufar Kwankwaso da Obi

  • Shugaban PDP na kasa ya dage cewa har gobe babu wata jam’iyya mafi girma a kaf nahiyar Afrika irin ta su
  • Umar Iliya Damagum ya kore tasirin jam’iyyun adawa kamar NNPP da LP har zuwa APC da ke rike da mulkin kasa
  • Ambasada Damagum da yake jagorantar NWC ya bude kofa ga tsofaffin ‘ya ‘yan da ke sha’awar dawowa PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Umar Iliya Damagum ya na ganin har yanzu babu jam’iyya a duk fadin kasashen Afrika duk da ta rasa mulki tun 2015.

Shugaban na jam’iyyar adawa ta PDP ya na ganin duk da rikicin cikin gidan da ya dabaibaye su, babu kamarsu a duk nahiyar nan.

Kara karanta wannan

"Abin da ya faru a zabukan 2015, 2019 da 2023" Inji shugaban jam’iyyar PDP

PDP APC
Shugaban PDP ya ce saboda a ci samu mukami aka kawo APC, NNPP da LP Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Babu jam'iyya kamar PDP a Afrika?

A hirar da jaridar Daily Trust ta yi da Ambasada Umar Iliya Damagum, ya ce ganin yadda PDP ta iya shanye rigingimu ya nuna karfinta.

Ya na ganin tun daga APC, NNPP zuwa LP babu wata jam’iyya kamar PDP, ya nuna cewa an kawo su ne domin samun mukaman siyasa.

‘Dan siyasar yake cewa fadi zabe ya na zuwa da kalubale wanda PDP ta ke gani a yau, abin da jam’iyyar APC ba ta taba fuskanta ba har yau.

"Duk da rikicin da aka fara a 2015, ba mu wargaje ba a matsayin jam’iyya ta PDP. Ina so in fito da wannan."
Sauran gungun – APC, NNPP da LP duk kame-kame ne. Ba asalin jam’iyyu ba ne, kafofin lashe zabe ne kurum.

Kara karanta wannan

PDP na neman birkicewa yayin da Wike ya sake kalulabantar gwamnonin jam'iyyar

- Ambasada Umar Iliya Damagum

Damagum ya haskawa duniya cewa APC ta na da gwamnoni 13 a jihohi da kusan rabin sanatoci da sauran kujerun majalisar tarayya.

Har wa yau, tsohon ‘dan takaran gwamnan na Yobe ya ce har jiga-jigan da ake ji da su yanzu a PDP, tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ne.

'Karshen APC ya zo' - Jam'iyyar PDP

Karfin PDP a kasar ne ya sa Damagum ya ce ana kokarin ganin wadanda suka sauya-sheka zuwa wasu jam’iyyun adawar sun dawo.

Babu wata mafita illa PDP domin kuwa an jarraba su a baya, a cewarsa mutane sun san karshen APC ya zo a matakan jihohi da kasa.

PDP ta ce ita ta ci zabukan 2019 & 2023

Ana da labari Umar Iliya Damagum ya zargi hukumar INEC da murde zabukan da aka yi a 2019 da kuma 2023 domin APC ta koma mulki.

Shugaban PDP ya hakikance cewa Muhammadu Buhari bai doke Atiku Abubakar a 2019 ba duk da ya yarda an yi kuskure a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng