Zaben Edo: Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game Manyan 'Yan Takara 3

Zaben Edo: Muhimman Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani game Manyan 'Yan Takara 3

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Zaben gwamnan jihar Edo na daya daga cikin abubuwan da za su ja hankalin a Najeriya a wannan shekarar da muke ciki 2024.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tsara gudanar da zaben gwamnan Edo a ranar 21 ga Satumba, 2024.

Asue Ighodalo, Monday Okpebholo da Akpata.
Abubuwan da ya dace ku sani game da ƴan takarar PDP, APC da LP a zaɓen Edo Hoto: @Aighodalo, @M_akpakomiza, @OlumideAkpata
Asali: Twitter

Yayin da zaɓen ke ƙara matsowa, Legit Hausa ta tattaro maku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da manyan ƴan takara uku.

Manyan 'yan takaran gwamna a zaben Edo

1. Asue Ighodalo (PDP)

Asuerinme Ighodalo lauya ne masanin doka kuma dan siyasa wanda ya fito daga ƙauyen Okaigben da ke yankin Ewohimi a ƙaramar hukumar Esan ta kudu maso Gabas a Edo.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi rashin nasara a rikicinsu da Ministan Shugaba Tinubu

Mista Ighodalo ya yi karatunsa na matakin farko a King's Collage da ke Legas, sannan ya gama digiri na farko a fannin ilimin tattalin arziki a jami'ar Ibadan a 1981.

Ya yi karatun zama lauya a makarantar lauyoyi ta Najeriya da ke Legas, inda ya gama a shekarar 1985. Daga nan ya fara aikin lauya.

A rahoton Bussiness Day, Ighodalo ya riƙe muƙamai da dama ciki har da shugaban daraktocin bankin Sterling, shugaban kamfanin fulawa na Ɗangote da sauransu.

Shi ne tsohon shugaban ƙungiyar NESG kuma ya yi aiki a hukumar kula da zuba jari ta Najeriya daga watan Mayu 2017 zuwa Mayu 2021.

Ighodalo ya yi murabus daga dukkan mukaman kamfani da ya rike saboda burin zama gwamnan Edo kuma ya samu nasarar zama ɗan takarar PDP a ranar 22 ga Fabrairu, 2024.

2. Sanata Monday Okpebholo (APC)

An haifi Okpebholo a ranar 29 ga Agusta 1970 a kauyen Udomi-Uwessan da ke ƙaramar hukumar Esan ta Tsakiya a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Ya yi makarantar firamare a Udomi, sannan ya fara karatun a makarantar sakandire ta Ujabhole duk a Esan da Tsakiya, ya ƙarisa a Jos, jihar Filato.

Monday Okpebholo ya yi digirinsa na farko a jami'ar Abuja kuma yanzu haka yana kokarin haɗa digiri na biyu a jami'ar ta Abuja.

A ɓangaren siyasa kuma, Okpebholo ya nemi takara kuma ya samu nasarar zama sanatan Edo ta tsakiya karkashin inuwar APC a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

A watan Fabrairu, 2024, Sanata Monday ya lashe zaɓen fitar da ɗan takara na jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Edo mai zuwa, Vanguard ta rahoto.

3. Olumide Akpata (LP)

An haifi Olumide Osaigbovo Akpata a ranar 7 ga watan Oktoba, 1972 a shiyyar Edo ta Kudu a jihar Edo.

Ya fara karatun firamare a Nana Primary School da ke Warri, sannan ya koma kwalejin gwamnatin tarayya ita ma a Warri, daga bisani ya koma King's Collage a Legas.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Masu neman takara 20 a NNPP sun fadi gwajin kwaya, NDLEA ta magantu

Akpata ya kammala digirin farko a fannin shari'a a jami'ar Benin, jihar Edo a 1992 sannan kuma ya zama cikakken lauya a Najeriya a 1993.

A ranar 30 ga Yuli, 2020, aka zaɓi Olumide Akpata a matsayin shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) bayan samun jimullar kuri'u 9,891.

Yanzu haka dai Mista Akpata shi ne ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar Edo da za a yi a ƙarshen makon gobe.

Gwamnan Edo Obaseki ya tona 'shirin' APC

A wani rahoton kuma gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa ana shirin cafke magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar.

Gwamna Obaseki ya yi zargin cewa APC na haɗa baki da ƴan sanda domin cafke jiga-jigan jam'iyyar PDP gabanin zaɓen gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262