An Soki Ɗan Majalisar Tarayya kan Raba Sandunan Rake a Matsayin Tallafi

An Soki Ɗan Majalisar Tarayya kan Raba Sandunan Rake a Matsayin Tallafi

  • Jam'iyyar PRP a jihar Bauchi ta caccaki dan Majalisar Tarayya game da raba sandunan rake a mazabarsa
  • PRP ta ce abin takaici ne yadda matar Hon. Aliyu Aminu Garu ke raba sandunan rake ga matasa a matsayin tallafi
  • Jam'iyyar ta kalubanci dan majalisar ya lissafo ayyukan alheri da ya yi wa mazabarsa tun bayan zuwansa Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - An yi ta ce-ce-ku-ce a kafofin sadarwa bayan matar dan Majalisar Tarayya a jihar Bauchi ta raba sandunan rake.

An yada hotunan ne yayin da matar dan Majalisar, Hon. Aliyu Aminu Garu da ke wakiltar mazabar Bauchi ke rabiyar a matsayin tallafi.

Kara karanta wannan

"Ya nuna jarumtaka": Atiku ya kadu da mutuwar babban sarki a kudancin Najeriya

An yi ta cece-kuce bayan dan Majalisar Tarayya ya raba sandunan rake a mazabarsa
Jam'iyyar PRP ta soki dan Majalisar Tarayya a Bauchi kan raba sandunan rake a matsayin tallafi. Hoto: Abdulrahman Sanusi.
Asali: Facebook

Bauchi: PRP ta caccaki dan Majalisar Tarayya

The Guardian ta ruwaito cewa lamarin ya jawo suka daga ɓangarori da dama ciki har da yan siyasa.

Jam'iyyar PRP a jihar Bauchi ta yi Allah wadai da irin wannan tallafi da aka ba wasu a mazabar.

Sakataren jam'iyyar a jihar, Abdulazeez Haruna ya bayyana hakan a matsayin abin kunya a gare su.

Haruna ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis 12 ga watan Satumbar 2024.

PRP a Bauchi ta kalubanci dan Majalisar Tarayya

"Ana yada wasu hotuna inda Hajiya Fatima Aminu Garu matar Hon. Aminu Garu ke raba sandunan rake ga matasa a matsayin tallafi."
"Wannan lamari bai kamata ba a ce dan Majalisar Tarayya yana raba sandunan rake ga yan mazabar Bauchi."

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

"A matsayinmu na jam'iyya, mun yadda cewa wakilci ya fi karfin raba wasu ƙananan abubuwa ga yan mazaba, mutane suna bukatar ababen cigaba ne ba wai irin wannan kaskanci ba."

- Abdulazeez Haruna

Jam'iyyar ta bukaci Hon. Garu ya bayyana abubuwan cigaba da ya kawowa al'ummar mazabarsa tun zuwansa Majalisa.

An bukaci Sanatan Bauchi ya nemi gwamna

A wani labarin, kun ji cewa bayan rasa sarautarsa a jihar Bauchi, an bukaci Sanata Shehu Buba ya nemi takarar gwamnan a zaben 2027.

Kungiyar Shehu Buba Umar Vanguard (SBUV) ta bayyana irin gudunmawa da Sanatan ya bayar a cigaban siyasar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.