Zaben Edo: APC Ta Fasa Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Zaben Edo: APC Ta Fasa Sanya Hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

  • Awanni kadan kafin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo, APC ta janye hannunta
  • A ranar 21 Satumba, 2024 ne za a gudanar da zaben gwamna a Edo, inda jam’iyyar PDP ta ce ta karaya da zaben
  • Gwamnan Edo, Godwin Obaseki da APC sun bayyana cewa ba su amince da yadda yan sanda ke gudanar da aikinsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Awanni biyu kacal kafin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben gwamnan Edo, APC ta janye daga shirin.

Wannan na zuwa awanni 12 bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya ce PDP ta karaya da yadda ta ga ‘yan sanda na gudanar da al’amuransu gabanin zaben.

Kara karanta wannan

NNPP ta fito da mace a matsayin 'yar takarar shugaban karamar hukumar Kano

Obaseki
APC ta janye daga yarjejeniyar zaman lafiya a Edo bayan zargin gwamnan jihar Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a ranar 21 Satumba, 2024 ne jama’ar Edo za su nufi mazabunsu domin zaben sabon gwamna a jihar.

APC ta janye daga yarjejeniyar zaman lafiya

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro cewa Jam’iyyar APC ta ce ba za ta amince ta sanya hannu kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya a jihar Edo ba saboda dalilan tsaro.

Jami’in hulda da jama’a na APC, Emperor Jarret Tenebe, ya zargi gwamna Godwin Obaseki da bayar da kariya ga mutanen da su ka kashe Sufeton yan sanda, Onuh Akor.

APC ta zargi yan sanda a Edo

Jam'iyyar APC a Edo ta zargi yan sanda da ke aiki a jihar da zama 'yan a-bi yarima a sha kida ga gwamna Godwin Obaseki saboda sun ki yin aikinsu.

APC ta bayyana cewa akwai wasu jagororin PDP da ke bugar kirji a bainar jama’a su na cewa babu abin da hukuma za ta iya yi idan sun aikata laifi.

Kara karanta wannan

"Za mu hargitsa komai": NLC ta yi barazana kan zaben dan takarar gwamnan PDP a bidiyo

Zanga zanga: APC ta zargi gwamnan Edo

A baya mun kawo labarin cewa jam'iyyar APC ta zargi gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da kasancewa daga cikin masu shirya zanga-zanga a Najeriya domin cimma manufarsa.

APC ta zargi gwamna Obaseki da kokarin haddasa rikici saboda a samu matsala a zaben jihar da ake shirin gudanarwa, da kuma jawo gagarumin rashin kwanciyar hankali a kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.