"Za Mu Hargitsa Komai": NLC Ta Yi Barazana kan Zaben dan Takarar Gwamnan PDP a Bidiyo
- Kungiyar NLC a Edo ta sake rura wutar rikici yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024
- Shugaban kungiyar, Odion Olaye ya nuna ƙarara yana goyon bayan dan takarar gwamna da jam'iyyar PDP ta tsaida, Asue Ighodalo
- Olaye ya ce idan har INEC ba ta sanar da Ighodalo ba a zaben da za a yi to za su hargitsa jihar baki dayanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Shugaban kungiyar NLC a jihar Edo, Odion Olaye ya tayar da kura kan zaben jihar da ake tunkara.
Olaye ya ce idan har ba a sanar da nasarar dan takarar PDP, Asue Ighodalo ba to komai zai iya faruwa a jihar.
Zaben Edo: NLC ta marawa PDP baya
Shugaban NLC ya fadi haka ne a faifan bidiyo da TVC News ta wallafa yayin kamfen Asue Ighodalo a Benin City.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olaye ya ce rigima da tashin hankali za su faru idan aka kuskura ba a sanar da Ighodalo wanda ya lashe zaben ba.
Kalaman Olaye sun sake tayar da hankulan jama'a yayin da ake dar-dar kan zaben da za a gudanar a jihar, cewar rahoton Daily Trust.
"Ina mai tabbatar muku PDP ce jam'iyyarmu kuma za ta yi nasara da 80% a zaben a ranar 21 ga watan Satumba."
"A ranar 22 ga watan Satumba za su sanar da Asue Ighodalo wanda ya yi nasara, idan INEC ba ta yi ba, to za mu rikita komai a Edo."
- Odion Olaye
Kalaman NLC ya sake rura wutar rikici
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024.
Har ila yau, ana zaman dar-dar duba da yadda jam'iyyun APC da PDP ke zargin juna kan shirin yin magudi a zaben da za a yi.
Obaseki ya yi fatali da bukatar Abdulsalami
Kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya yi fatali da bukatar tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar kan zabe.
Abdulsalami ya bukaci gwamnan ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin zaben gwamnan da za a yi a Edo.
Sai dai gwamnan ya ce ba zai sanya hannu a yarjejeniyar ba saboda babu alamun zaman lafiya bayan cafke 'yan PDP 60.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng