Zaben Edo: Kotu Ta Yi Hukunci kan Sahihancin Tikitin 'Dan Takarar Gwamna
- Kotun ɗaukaka ƙara ta zartar da hukunci kan ƙarar da ke neman soke tikitin takarar gwamna na Olumide Akpata a ƙarƙashin jam'iyyar LP
- Alkalai sun yi watsi da ƙarar da Kenneth Imansuangbon ya shigar inda ya nemi a soke tikitin takarar gwamnan da aka damkawa Olumide Akpata
- Kotu ta ce mai shigar da ƙarar ya kasa gabatar da sahihan hujjoji kan iƙirarin da ya yi na cewa ba a ba shi sakamakon zaɓen fidda gwanin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta yi hukunci kan ƙarar da ke neman soke tikitin takarar gwamnan Edo na Olumide Akpata.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da ke neman soke tikitin takarar na ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar da za a a yi a ranar, 21 ga watan Satumban.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 11 ga watan Satumban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa kotu ta yi watsi da ƙarar
A hukuncin bai ɗaya da suka yanke, alƙalan kotun guda uku sun amince cewa wanda ya shigar da ƙarar, Kenneth Imasuangbon, bai bi hanyoyin warware rikici da jam'iyyar take da su ba kafin ya garzaya kotu.
A hukuncin da mai shari'a Okon Abang ya gabatar, kotun ta bayyana cewa ƙarar ba ta kawo sahihan hujjoji ba kan wanda ake ƙara, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Kotun ta bayyana cewa iƙirarin da Imasuangbon ya yi na cewa jam'iyyar LP ba ta ba shi sakamakon fidda gwanin ba, bai inganta ba saboda akwai wakilin shi a wajen zaɓen.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma nuna kuskuren Imasuangbon wajen gaza kiran wani shaida ko deliget daga cikin waɗanda ya yi iƙirarin sun zaɓe shi a zaɓen fidda gwanin.
Ɗan takarar gwamnan Edo ya kwafsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamna a jihar Edo karkashin APC, Monday Okpebholo ya tafka kuskure wajen yaƙin neman zaɓe.
Monday Okpebholo yayin yaƙin neman zaɓen a jihar ya yi suɓutar baki inda ya yi alƙawarin kawo wa al'umma 'rashin tsaro' idan suka zaɓe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng