Tsohon Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Hasashen Makomar Shugaba Tinubu a 2027

Tsohon Mataimakin Shugaban APC Ya Yi Hasashen Makomar Shugaba Tinubu a 2027

  • Tsohon mataimakin shugaban APC ya bayyana dailin da zai sa ƴan Najeriya su kayar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027
  • Salihu Lukman ya ƙara caccakar gwamnati mai ci, yana mai cewa sha'anin tsaro da tattain arziki sun ƙara taɓarɓarewa a mulkin Tinubu
  • Ya ce jam'iyyar APC ta kunyata ƴan Najeriya, inda ya ce a shirye yake ya marawa shugaban kasar baya idan har ya gyara kuskurensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su farka daga barci.

Lukman ya ce kamar yadda ƴan Najeriya suka kawar da mulkin sojoji shekaru 25 da suka wuce, za su kawo ƙarshen mulkin Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

2027: Kiran Kwankwaso, Atiku da Obi su tararwa Tinubu ya fusata jam'iyyar APC

Shugaba Tinubu da Salishu Lukman.
Salihu Lukman ya sake sukar salon mulkin Tinubu, ya ce ƴan Najeriya za su kayar da shi a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Salihu Lukman
Asali: Facebook

Najeriya ta sake shiga matsala a mulkin Tinubu

Ya yi wannan furucin ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2024.

Tsohon jigon APC ya ce matsalar tsaro a Najeriya da tattalin arziki sun tabarbare a cikin watanni 15 da suka gabata karkashin Shugaba Tinubu.

Salihu Lukman ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta ba ƴan Najeriya kunya kuma ba ta cancanci mutane su sake dangwala mata a zaɓe na gaba ba.

Lukman ya hango makomar Tinubu a 2027

"Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a haka ba a kasar nan, dole mu yi sadaukarwa wataƙila hakan ya zama sanadin kawo canji, she ne babban burina a yanzu.
“Ina da tabbacin kuma ina da yakinin cewa yadda muka samu nasarar kawar da sojoji daga mulki, za mu gyara kuskuren da muka yi da matsalar da ke faruwa a yanzu.

Kara karanta wannan

A ƙarshe Shugaba Tinubu ya faɗi ayyukan da yake yi da kudin tallafin man fetur

"APC da Shugaba Asiwaju Tinubu za su sha mamaki a 2027, za mu zaɓi shugabannin da za su zama tamkar bayi ga ƴan ƙasa, ba irin na yanzu masu ƙarfin iko ba."

- Salihu Lukman.

Lukman ya gindaya sharaɗin goyon bayan Tinubu

Tsohon Darakta-Janar na kungiyar gwamnonin APC ya ce Tinubu na cikin waɗanda suka ci moriyar dawowar damokuraɗiyya, ya kamata ya yi abin kirki.

Lukman ya ce idan har Shugaba Tinubu ya koma baya ya yi abin da ya dace, zai ba shi hakuri kuma ya marawa gwamnatinsa baya, rahoton Ripples Nigeria.

APC ta ɗauki zafi game da kalaman Lukman

A wani rahoton kuma APC mai mulki ta mayar da zazzafan martani ga Salihu Lukman, tsohon mataiamkin shugaba a Arewa maso Yamma.

Mai magana da yawun APC, Felix Morka ya ce Lukman na ƙoƙarin ɗauke hankalin jama'a daga ayyukan alherin da Bola Tinubu yake yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262