"Mene Suke Fada Maka": Shugaban Yarbawa Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Manyan Abokansa 2

"Mene Suke Fada Maka": Shugaban Yarbawa Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Manyan Abokansa 2

  • Jagoran Yarbawa a yankin Kudu maso Yamma, Gani Adams ya koka kan yadda tsare-tsaren Bola Tinubu ke kuntatawa al'umma
  • Gani Adams ya bukaci shugaban da ya yi gaggawar janye wasu daga cikin tsare-tsaren da suka jefa al'umma cikin mawuyacin hali
  • Ya kuma shawarci Tinubu ya kori gwamnan CBN, Yemi Cardoso da ministan kudi, Wale Edun kan rashin kawo sauyi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Sarkin Yakin shugabannin Yarbawa, Gani Adams ya caccaki wasu mukarraban Shugaba Bola Tinubu.

Gani Adams ya bukaci Tinubu ya sallami wasu daga cikin wadanda ya nada mukamai daga yankin saboda rashin katabus.

An shawarci Tinubu ya sallami wasu daga cikin na hannun damansa
Sarkin Yakin Yarbawa, Gani Adams ya bukaci Bola Tinubu ya janye tsare-tsarensa da suka jawo kunci. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Gani Adams ya caccaki tsare-tsaren Tinubu

Kara karanta wannan

'Ka ba mu kunya:' Shugaban Yarabawa ya tura zazzafar wasika ga Tinubu

Dattijon ya fadi haka ne a cikin wata wasika da ya rubutawa Tinubu, kamar yadda da Channels TV ta ruwaito.

Gani Adams ya caccaki tsare-tsaren shugaban game da yadda ake gudanar da tattalin arzikin kasar.

Ya ce bai san menene gwamnan CBN, Yemi Cardoso da Ministan kudi, Wale Edun ke yi a gwamnatin ba, cewar rahoton Vanguard.

An bukaci Tinubu ya janye wasu matakai

Har ila yau, Gani Adams ya koka kan yadda shugaban ya ke cigaba da kuntatawa al'umma da tsare-tsarensa na tattalin arziki.

Daga bisani ya bukaci Tinubu da ya yi gaggawar janye wasu matakai da ya dauka domin saukakawa al'umma.

"Yanzu wandada su ne na hannun damanka tun kana gwamnan Lagos daga shekarar 1999 zuwa 2007 su ne ke kula da tattalin arziki."

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

"Wadannan mutane guda biyu sun hada da Ministan kudi, Wale Edun da gwamnan babban bankin CBN, Yemi Cardoso."

Gani Adams

Gani Adams ya soki Tinubu kan rashin katabus

Kun ji cewa shugaban Yarabawa na Aare Ina Kakanfo, Gani Adams ya tura wasika mai zafi ga Bola Tinubu.

Iba Gani Adams ya tura wasikar ne yana kokawa kan yadda rayuwa ta yi tsanani a Najeriya musamman ga talakawa.

Gani Adams ya ce a lokacin da Bola Tinubu ya ci zaɓe a 2023 an yi tsammanin zai tabuka abin kirki a Najeriya kamar jihar Lagos.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.