Zaben Edo: Gwamna Obaseki Ya Fallasa Makarkashiyar da Ake Yiwa PDP
- Gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa ana shirin cafke magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar
- Obaseki ya yi zargin cewa APC na haɗa baki da ƴan sanda domin cafke jiga-jigan PDP gabanin zaɓen gwamna
- Zargin na gwamnan na zuwa ne yayin da ya rage sauran ƴan kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa akwai wani shiri na cafke ƴaƴan jam’iyyar PDP gabanin zaɓen bana.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta tsayar da ranar 21 ga watan Satumba domin gudanar da zaɓen na gwamna a jihar.
A wani rubutu a shafinsa na X a ranar Talata, Obaseki ya ce shirin da ake yi na kama mambobin PDP barazana ne ga dimokuradiyyar ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi Gwamna Obaseki ya yi?
Gwamna Obaseki ya yi zargin cewa jam'iyyar APC na haɗa kai da ƴan sanda domin cafke mambobin PDP ta yadda za a samu rikici a jihar gabanin zaɓen gwamna.
"Na samu tabbaci cewa shirin shi ne a cafke manyan jiga-jigan PDP masu yawa. Wannan abu ne mai matuƙar hatsari kuma barazana ga dimokuraɗiyyarmu."
"Sam bai dace ba yadda aka cafke shugaban ƙaramar hukumar Esan ta Yamma aka tafi da shi zuwa Abuja, wanda hakan cin fuska ne ga iko na a matsayin babban jami'in tsaro na jiha."
"Ina kira da babbar murya ga magoya bayan PDP da su kwantar da hankulansu su zauna cikin lumana."
- Gwamna Godwin Obaseki
Gwamna Obaseki ya ce zai miƙa ƙorafinsa ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun.
APC ta zargi Gwamna Obaseki
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen Edo ta zargi Gwamna Godwin Obaseki da shirya gagarumar zanga-zangar da za ta rikita jihar ranar 15 ga watan Satumba, 2024.
Bayan haka, APC ta kuma yi zargin cewa gwamnan ya fara kulle-ƙullen yadda zai haɗa kai da sauran gwamnonin PDP domin kawo hargitsi a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng