Ministan Buhari da Wasu Mutane 6 da Ake Hasashen Za Su Maye Gurbin Ajuri Ngelale

Ministan Buhari da Wasu Mutane 6 da Ake Hasashen Za Su Maye Gurbin Ajuri Ngelale

Tun bayan ajiye aiki da hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale ya yi, an fara hasashen maye gurbinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wasu sun fara bayyana wadanda suke ganin Shugaba Tinubu zai iya yin amfani da su a mukamin mai magana da yawunsa.

Wadanda ake hasashe za su gaji kujerar Ajuri Ngelale
Mutane 7 da Ake Hasashen Za Su Gaji Kujerar Ajuri Ngelale. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Wa zai canji Ajuri Ngelale?

Ngelale ya ajiye mukamin kakakin shugaban ne a ranar Asabar 7 ga watan Satumbar 2024 saboda dalilin kula da rashin lafiyar iyalansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta leko wadanda ake tunanin za su iya maye gurbin Ngelale:

1. Daniel Bwala

Daniel Bwala shi ne tsohon hadimin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Maganar Sheikh Jingir da wasu abubuwa da suka tayar da kura kan gwamnatin Tinubu

Daga bisani ya watsar da Atiku inda ya koma goyon bayan Tinubu a fili wanda ya sa ake tunanin shugaban zai iya saka masa da mukamin.

2. Bayo Onanuga

Bayo Onanuga shi ne wanda ke rike da mukamin hadimin shugaban bangaren yada labarai da tsare-tsare.

Onanuga shi ne tsohon daraktan hukumar NAN yana da kusanci da Tinubu da ake ganin zai iya ba shi mukamin.

3. Tolu Ogunlesi

Tolu Ogunlesi ya kasance daga cikin wanda ake sa ran za su samu mukamin kakakin Bola Tinubu bayan ajiye aiki da Ngelale ya yi.

Ogunlesi shi ne tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bangaren sadarwa ta zamani.

4. Sunday Dare

Tsohon Ministan wasanni a mulkin Muhammadu Buhari, Sunday Dare na cikin wadanda ake sa ran su gaji mukamin Ngelale.

An yi ta hasashen bayan Tinubu ya dare mulki zai nada Dare mukamin Minista amma hakan bai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: Kura kurai 2 da suka sa hadimin Tinubu ya ajiye aikinsa

5. Tunde Rahman

A yanzu haka Tunde Rahman shi ne hadimin Tinubu a bangaren sadarwa bayan ya rike mukamin ga shugaban kafin a zabe shi.

6. Temitope Ajayi

Kaman Tunde, shi ma Ajayi hadimi ne ga Bola Tinubu a bangaren sadarwa da yada labarai.

Ajayi ya yi aiki da Tinubu tun lokacin kamfen zaben 2023 wanda ya dade tare da shugaban a bangaren sadarwa.

7. Otega Ogra

A watan Yulin 2023, Shugaba Bola Tinubu ya nada Ogra a matsayin hadiminsa a bangaren sadarwa ta zamani.

A baya, Ogra ya yi aiki a bankunan Najeriya kafin ya koma aiki da kamfanin BUA na Abdussamad Rabiu.

An fadi 'dalilin' Ngelale na ajiye aiki

Kun ji cewa wasu rahotanni sun tabbatar da cewa hadimin Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki ne saboda kokarin korarsa da ake yi.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce ana ƙoƙarin kwace muƙamin Ngelale na kakakin shugaban kasa saboda rashin kwarewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.