Zaɓen Kano Ya Gamu da Cikas, Majalisar Dokoki Ta Ɗauki Mataki kan Ciyamomi 44

Zaɓen Kano Ya Gamu da Cikas, Majalisar Dokoki Ta Ɗauki Mataki kan Ciyamomi 44

  • Shugabannnin kananan hukumomi 44 na riko a Kano za su ci gaba da zama kan mulki har zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, 2024
  • Majalisar dokokin Kano ta amince da tsawaita wa'adin kantomomin da watanni biyu a zamanta na ranar Litinin, 9 ga watan Satumba
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake tunkarar zaɓen kananan hukumomi wanda aka tsara yi a watan Oktoban mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da tsawaita wa’adin shugabannin kananan hukumomi 44 na riko da watanni biyu.

Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne bayan mataimakin gwamna kuma kwamishinan ƙananan hukumomi, Abdulsalam Gwarzo ya miƙa bukatar hakan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wani asibiti a Kaduna, sun tafka ɓarna

Majalisar dokokin jihar Kano.
Majalisar dokokin Kano ta tsawaita wa'adin kantomomi 44 da watanni 2 Hoto: Kano State Assembly
Asali: Facebook

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala shi ne ya karanta wasiƙar mataimakin gwamnan a zaman yau Litinin, Leadership ta rahoto.

Meyasa majalisar Kano ta ɗauki matakin?

Ƙarin wa'adin da aka yi wa kantomomin zai fara aiki ne daga ranar 9 ga watan Satumba, 2024 zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, 2024.

Wannan mataki da majalisar ta ɗauka ya zama kusan tilas sakamakon ƙarewar wa'adin kantomomin kananan hukumomin jiya Lahadi, 8 ga Satumba.

A wata hira da manema labarai bayan zaman majalisar, Lawan ya bayyana cewa kantomomin za su sauka daga muƙamansu da zarar an rantsar da zaɓaɓɓun ciyamomi.

Kotu ta sa baki a zaɓen Kano

Rahotanni sun nuna cewa zaɓen kananan hukumomin jihar Kano da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga watan Oktoba, 2024 na fuskantar ƙalubalen shari'a.

Kara karanta wannan

"Ku taimake mu": Gwamna a Arewa ya sallami shugabannin kananan hukumomi 17

A ranar 4 ga watan Satumba, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta haramtawa hukumar zaɓen Kano (KANSIEC) karɓan N10m da N5m a matsayin kuɗin takara.

KANSIEC ta ƙayyade N10m a matsayin kuɗin tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma da N5m a matsayin kuɗin takarar kansila, amma kotun ta dakatar da hakan.

Mai shari’a Emeka Nwite ya dakatar da karbar kuɗin takarar har sai an yanke hukunci a ƙarar da jam'iyyun SDP, APP da ADP suka shigar, wanda aka tsara ranar 25 ga Satumba, 2024.

Tsawaita wa'adin kantomomin da majalisa ta yi zai ba da damar ci gaba da tafiyar da harkokin ƙananan hukumomi duk da rashin tabbacin zaɓen da ke tafe, rahoton Channels tv.

Gwamnatin Kano ta ƙaɗa hutun makarantu

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta sanar da ɗaukar matakin ɗage ranakun da za a koma makarantun firamare da na gaba da su a jihar.

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

Ma'aikatar ilmi ta jihar wacce ta sanar da ɗage ranakun komawa makarantar ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda wasu dalilai na gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262