Ganduje da APC Sun Yi Rashi, Tsohon 'Dan Majalisa Ya Koma PDP
- Bayan ya tattara komatsansa ya fice daga jam'iyyar APC, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo ya sauya sheƙa zuwa PDP
- Honarabul Emmanuel Agbaje ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa PDP ne bayan ya kammala shawarwari a cikin tsanaki
- Tsohon ɗan majalisar ya samu tarba daga jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar bayan ya yanke shawarar komawa cikinta a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo na jam'iyyar APC ya sauya sheƙa zuwa PDP.
Honarabul Emmanuel Agbaje ya koma jam'iyyar PDP ne kwanaki kaɗan bayan ya fice daga jam'iyyar APC.
APC ta yi rashi, jam'iyyar PDP ta dace
Jaridar Vanguard ta ce ya samu tarba a mazaɓar a Ososo ta 10 a yayin wani gangamin PDP da aka shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin gwamnan jihar, Marvelous Omobayo, shugaban ƙaramar hukumar Akoko-Edo, Honarabul Tajudeen Alade da sauran jiga-jigan PDP ne suka tarbi tsohon jigon na APC.
Meyasa Agbaje ya koma jam'iyyar PDP?
A nasa ɓangaren, Emmanuel Agbaje ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP ne saboda jam’iyyar ce ke da burin taimakawa mutanen Akoko-Edo.
"Ba bisa kuskure muka zo nan ba, mun zo nan ne bayan shawarwarin da muka yi a tsanake. Mun kalli dukkanin jam’iyyun, mun zaɓi wacce take da muradin kyautatawa al’ummarmu."
"A karon farko a tarihin Akoko-Edo, muna da mataimakin gwamna, muna son cin gashin kanmu, muna son gwamnatin da za ta saurare mu, mun gaji da jam’iyyar da ke yi mana ƙarya shi ya sa muka zaɓi PDP."
- Honarabul Emmanuel Agbaje
Karanta wasu labaran kan APC
- "Za mu kawo muku rashin tsaro ": Ɗan takarar gwamna a APC ya kwafsa a bidiyon kamfe
- Ganduje zai bar APC": Malami ya yi hasashen rikici tsakanin Tinubu da Shettima
- Ganduje ya girgiza 'yan adawa, ya fadi shirin APC na kwace jihohin Najeriya
APC ta fasa shiga zaɓen ciyamomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta janye daga shiga zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a ranar, 21 ga watan Satumban 2024.
APC ta cimma matsayar ƙin shiga cikin zaɓen ne yayin taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a birnin Awka, babban birnin jihar a ranar Asabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng