"Ba Rashin Lafiya ba ne": An Fadi Ainihin 'Dalilin' Ajuri Ngelale Ajiye Aikinsa a Abuja

"Ba Rashin Lafiya ba ne": An Fadi Ainihin 'Dalilin' Ajuri Ngelale Ajiye Aikinsa a Abuja

  • Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa hadimin Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki ne saboda kokarin korarsa da ake yi
  • Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce ana ƙoƙarin kwace muƙamin Ngelale ne na kakakin shugaban kasa saboda rashin kwarewa
  • Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da Ajuri Ngelale ya yi da cewa zai kula da rashin lafiyar iyalansa da ya yi kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Bayan murabus din hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Ajuri Ngelale, wasu rahotanni sun fara fitowa.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ba maganar rashin lafiya ba ce, akwai wani shiri na tuge shi daga mukamin nasa.

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale: Tinubu ya yi magana bayan hadiminsa ya ajiye aiki, ya dauki mataki

An fadi wasu 'dalilai' da ya tilasta Ngelale ajiye aikinsa
Wasu majiyoyi sun fadi 'dalilin' ajiye aiki da Ajuri Ngelale ya yi. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Ngelale: Bayanai kan ajiye aikin hadimin Tinubu

Premium Times ta samu wasu rahotanni da ke nuni da cewa fadar shugaban kasa ta fara neman wanda zai maye gurbinsa saboda rashin katabus.

Ngelale ya na rike da mukamin mai magana da yawun shugaban kasa da kuma wakilin Shugaban ƙasa na musammman kan sauyin yanayi.

An ruwaito cewa Tinubu ya bukaci Ngelale ya kula da bangarensa na wakili a sauyin yanayi domin maye gurbinsa na kakakin shugaban kasa.

Sai dai Ngelale ya karkara wurin rike muƙamin kakakin shugaban da kuma shirin ajiye mukaminsa na bangaren sauyin yanayi.

An tabbatarwa Ngelale cewa zai iya kasancewa a bangaren sadarwa amma za a naɗa wani ya zama shugabansa.

Rashin ganin Tinubu ya rikita Ajuri Ngelale

Wata majiya ta ce hakan ya jawo matsala wanda har aka hana Ngelale ganin shugaba Tinubu na wasu makwanni.

Kara karanta wannan

Babban hadimin Shugaba Tinubu ya ajiye aikinsa, ya jero dalilai masu ƙarfi

Har ila yau, wasu rahotanni sun tabbatar da cewa an nada Ngelale a mukaminsa ne bayan ba da sunansa da ɗan shugaban kasa ya yi wato Seyi Tinubu.

"Rashin lissafi ne a ce Tinubu ya nada karamin dan jarida a wannan matsayi mai daraja, shi yasa bai tabuka abin a zo a gani ba."

- Cewar wata majiya

Tinubu ya amince da murabus din Ngelale

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da karbar takardar murabus da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya yi a jiya Asabar.

Tinubu ya godewa Ngelale game da gudunmawar da ya bayar yayin da yake aiki tare da yi masa fatan alheri da kuma iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.