"Jana'iza ce Ta Haɗa Mu": Gwamna Ya Fadi Silar Kaurewa Tsohon mai Gidansa

"Jana'iza ce Ta Haɗa Mu": Gwamna Ya Fadi Silar Kaurewa Tsohon mai Gidansa

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya fadi ainihin abin da ya haɗa shi da Adams Oshiomhole
  • Obaseki ya ce kawai domin ya shirya jana'iza ta musamman ga jigon PDP, Cif Tony Anenih shi ne ya batawa Oshiomhole rai
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kamfen zaben gwamnan jihar da za a yi a watan Satumbar 2024 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fadi dalilin fadansu da tsohon Gwamna, Adams Oshiomhole.

Obaseki ya ce jana'izar jigon PDP, Cif Tony Anenih ne ya hada su fada saboda Oshiomhole ba ya so.

Kara karanta wannan

Babban hadimin Shugaba Tinubu ya ajiye aikinsa, ya jero dalilai masu ƙarfi

Gwamna ya fadi silar samun matsalarsa da mai gidansa Oshiomole
Gwamna Godwin Obaseki ya fadi dalilin fadansu da Adams Oshiomole. Hoto: Godwin Obaseki, Adams Oshiomole.
Asali: Facebook

Edo: Dalilin fadan Obaseki da Oshiomhole

Punch ta ruwaito Obaseki na fadin haka yayin kamfe a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jiya Asabar 7 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce Oshiomole bai ji dadin shirya jana'izar Anenih da gwamnatin jihar ta yi ba da cewa hakan kuskure ne.

Obaseki ya ce yaki amincewa da abin da Oshiomhole ke so musamman kan shirya jana'izar dattijon a jihar, Vanguard ta ruwaito.

"Jana'iza ce ta haɗa mu da Oshiomhole" - Obaseki

"Lokacin da Cif Tony Anenih ya rasu, a matsayina na dan APC a lokacin na tabbatar da yi masa jana'iza ta musamman wanda hakan ne ya hada ni fada da Oshiomhole."
"Oshiomhole ya ce Anenih ba shi da wani matsayi a jihar me yasa zan yi masa haka, na ce ai Anenih ya fi wasu gwamnonin amfani, saboda haka ya cancanta."

Kara karanta wannan

Ana kuka da tsadar mai, Gwamna a Arewa ya cire tuta wurin kawowa al'umma sauki

- Godwin Obaseki

Gwamna Obaseki ya dakatar da bude makarantu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Edo ta ba da sabuwar sanarwar kan bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu.

Gwamnatin ta umarci dakatar da bude makarantun da aka shirya a ranar 9 ga watan Satumbar 2024 har sai baba ta gani

Wannan na zuwa ne bayan kara farashin mai da kamfanin NNPCL ya yi wanda ya sake jefa al'umma cikin matsi da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.