Ana Dab da Fara Kada Kuri'a, APC Ta Janye daga Shiga Zaben Ciyamomi

Ana Dab da Fara Kada Kuri'a, APC Ta Janye daga Shiga Zaben Ciyamomi

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a jihar ba
  • APC ta bayyana cewa za ta shigar da ƙara a gaban kotu idan har hukumar zaɓen jihar ta gudanar da zaɓen
  • APC ta bayyana cewa za ta buƙaci kotun ta soke zaɓen domin ya saɓawa dokar zaɓe ta 2022 wacce aka yiwa garambawul

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Jam'iyyar APC reshen jihar Anambra ta janye daga shiga zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Anambra (ANSIEC) ta tsayar da ranar, 28 ga watan Satumban 2024 domin gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta taso masu POS a gaba, za a fara kulle masu shaguna

APC ta fasa shiga zabe a Anambra
APC ta janye daga shiga zaben ciyamomi a Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

APC ta janye daga zaɓen Anambra

Jaridar Tribune ta rahoto cewa jam'iyyar ta sanar da cewa za ta kai ƙarar hukumar zaɓen kan abin da ta kira rashin bin tsarin doka wajen shirya zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta cimma matsayar ƙin shiga cikin zaɓen ne yayin taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a birnin Awka, babban birnin jihar a ranar Asabar.

Jam'iyyar ta ce za ta buƙaci kotun ta soke zaɓen idan har hukumar ANSIEC ta gudanar da shi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Meyasa APC ta janye daga zaɓen?

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa shiga cikin zaɓen zai zama yarda a yiwa dimokuraɗiyyar Najeriya karan tsaye.

APC ta nuna cewa sashe 23(1) na dokar ANSIEC ta 2024, wanda ya ba da damar sanar da zaɓe kwana 30 kafin a fara a matsayin wanda bai cancanta ba saboda ya saɓa sashe 103(3) na dokar zaɓe ta 2022, wanda ya ba da damar sanar da zaɓe kwana 150 kafin a fara.

Kara karanta wannan

TUC ta yi fatali da ƙarin farashin man fetur, ta aika sakon gaggawa ga Bola Tinubu

Sun buƙaci kotun da ta hana ANSIEC daga gudanar da zaɓen a ƙananan hukumomi 21 na jihar.

APC ta samu koma baya a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu koma baya a jihar Edo ana saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

Jigo a jam'iyyar kuma tsohon ɗan majalisar dokokin jihar wanda ya wakilci Akoko-Edo II daga 2015 zuwa 2023, Honarabul Emmanuel Agbaje ya yi murabus daga zama mamba a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng