2027: Malamin Addini Ya ba Jonathan Shawara kan Tsayawa Takara, Ya Fadi Abin da Zai Faru

2027: Malamin Addini Ya ba Jonathan Shawara kan Tsayawa Takara, Ya Fadi Abin da Zai Faru

  • Yayin da ake ta kiran tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara, Fitaccen Fasto a Najeriya ya ba shi shawara
  • Fasto Elijah Ayodele ya shawarci Jonathan da ka da ya kuskura ya sake maganar tsayawa takarar shugaban kasa a 2027
  • Wannan na zuwa ne yayin ake ta kiran tsohon shugaban da ya fito neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Fitaccen Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya yi magana kan takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Ayodele ya gargadi Jonathan kan sake tunanin tsayawa takara a zaben shugaban kasa a 2027.

Malamin addini ya gargadi Jonathan kan tsayawa takara a zaben 2027
Fasto Elijah Ayodele ya shawarci Goodluck Jonathan kan sake tsayawa takarar shugaban kasa. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

2027: An shawarci Jonathan kan takara zabe

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa bai kamata Goodluck Jonathan ya sake neman takara a 2027 ba'

Faston ya bayyana haka ne a cikin faifan bidiyo a shafinsa na X a jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya ce bai kamata Jonathan ya biyewa masu neman tunkuda shi tsayawa takara ba a 2027.

Ya bukaci tsohon shugaban da ya rike mutuncinsa da kare martabar da ya ke da shi a kasar.

"Jonathan kada ka tsaya takara a zaɓen 2027, idan ka sake tsayawa za ka bata sunanka gaba daya."
"Ka da ka bari yan siyasa su yaudare ka sake tsayawa takara, ka yi abin kirki lokacin da kake ofis, don Allah ka da ka sake tsayawa."

- Elijah Ayodele

Wannan na zuwa ne yayin da wasu ke kiran tsohon shugaban da ya sake dawowa neman kujerar shugaban kasar da za a yi zabe a shekarar 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Kun matsawa masu zanga zanga maimakon 'yan ta'adda," Atiku ya caccaki Tinubu

Sai dai ana ta ba Jonathan shawara kan ya yi fatali da kiraye-kirayen domin kare mutuncinsa a kasar.

2027: An shawarci Jonathan kan tsayawa takara

Kun ji cewa wata kungiyar mata da kananan yara ta shawarci tsohon shugaban kasa, Gooduck Jonathan kan neman takara a 2027.

Kungiyar ta ce ya kamata Jonathan ya tsaya matsayinsa na dattijo ba tare da tsunduma a harkokin siyasa ba a yanzu.

Shugaban kungiyar, Ogoegbunam Kingdom shi ya tabbatar da haka yayin da ya ke zantawa da jaridar Legit a wannan mako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.