Jigo a PDP Ya Ba Shugaban Jam'iyyar Mafita kan Rikicin da Take Ciki

Jigo a PDP Ya Ba Shugaban Jam'iyyar Mafita kan Rikicin da Take Ciki

  • Tsohon sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar PDP, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar
  • Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa idan har ana son a warware rikicin dole ne sai muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus
  • Ya bayyana cewa murabus ɗin Umar Damagum zai sanya a samu damar warware rikicin da ya addabi jami'yyar ta adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya yi kira ga muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum, ya yi murabus.

Kola Ologbondiyan ya buƙaci Umar Damagum ya yi murabus daga muƙaminsa ne domin a warware rikicin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yiwa ministocinsa

Jigo a PDP ya bukaci Damagum ya yi murabus
Jigo a PDP na son Damagum ya yi murabus daga mukaminsa Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

An taso shugaban PDP a gaba

A wata hira da jaridar The Punch, Ologbondiyan ya bayar da hujjar cewa murabus ɗin Damagum zai ba da damar yin garambawul da kuma dawo da zaman lafiya a PDP.

Ologbondiyan ya ɗora alhakin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a kan Damagum, inda ya jaddada cewa idan har ana son warware rikicin, dole sai muƙaddashin shugaban ya yi murabus.

Ya bayyana cewa idan har ana son a yi sulhu na gaskiya, dole ne sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa ya fito daga shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Ologbondiyan ya ce an hana shiyyar muƙamin ne tun bayan dakatar da Iyorchia Ayu daga shugabancin jam'iyyar.

Meyasa ake son Damagum ya yi murabus?

"Babu wata muhawara da za a yi kan cewa idan har PDP na son cimma burikanta, dole ne sai an yi gaskiya da adalci. Damagum ya riƙe muƙamin da ya kamata a ce ya fito daga shiyyar Arewa ta Tsakiya."

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya shiga matsala bayan ya yi wa wasu gwamnoni barazana

"Idan da a ce ya tsaya a ofishinsa sannan ya bari shiyyar Arewa ta Tsakiya ta samar da shugaba, da tuni an warware manyan matsalolin da suka addabi jam'iyyar.

- Kola Ologbondiyan

Damagum ya ɗage taron NWC na PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban riƙo na ƙasa na PDP, Umar Damagum ya dage babban taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar zuwa mako mai zuwa.

Damagum ya ɗage taron ne saboda ƙaruwar takun saka tsakanin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da kungiyar gwamnonin PDP, dangane da matsayin zaben jam'iyyar na Ribas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng