Jerin Sanatoci 10 da Suke Karɓan Albashi na Musamman Duk Wata a Majalisa

Jerin Sanatoci 10 da Suke Karɓan Albashi na Musamman Duk Wata a Majalisa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A ƴan makonnin nan an yi ta surutu kan adadin kuɗin da ake biyan kowane sanata a matsayin albashi a ƙarshen wata a Najeriya.

Makudan kuɗin da ƴan majalisar tarayya suke laƙumewa a kowane wata ya ja hankalin ƴan Najeriya duba da halin ƙunci da yunwar da ake fama da ita a ƙasar nan.

Barau I Jibirin, Akpabio da Bamidele.
Manyan sanatoci 10 da suke ɗaukar albashi na musamman a wata Hoto: @barauijibrin, @SPNigeria, @Mob_sen_leader
Asali: Twitter

Yayin da sanatoci 99 daga cikin 109 ke samun kusan N2.079bn duk wata, har yanzun ba a tantance adadin kuɗin da ragowar sanatoci 10 suke karɓa ba duk wata.

An tattara alkaluman kuɗin da sanatoci ke karɓa ne bisa la'akari da kalaman Sanata Kawu Sumaila (NNPP, Kano ta Kudu), wanda ya ce yana samun N21m a wata, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ba Tinubu shawarar abin da ya kamata ya yiwa ministocinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Sanata Kawu Sumaila ya gaza tantance ainihin albashin da shugabanni a majalisar dattawa ta 10 ke samu.

Duk wani ƙoƙari na gano gaskiyar abin da sauran sanatoci 10 ke laƙumewa a wata bai yi nasara ba, har tsofaffin sanatoci sun ce ba su san ainihin albashi da alawus ɗin shugabannin majalisa ba.

Legit Hausa ta tattaro maku jerin waɗannan sanatoci 10 da suke karban kunshin albashi na musamman a Najeriya.

1. Godswill Akpabio

Sanata Godswill Akpabio, shi ne shugaban majalisar dattawa ta 10 kuma lamba ɗaya a cikin sanatoci, yana wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Ya riƙe muƙamai da dama a tarihin siyasarsa wanda ya haɗa da gwamnan jihar Akwa Ibom na tsawon zango biyu da kuma minista a mulkin Muhammadu Buhari.

2. Barau I. Jibrin

Sanata Barau shi ne lamba biyu a majalisar dattawa, shi ne wakilin al'ummar Kano ta Arewa a majalisa ta 10.

Kara karanta wannan

TUC ta yi fatali da ƙarin farashin man fetur, ta aika sakon gaggawa ga Bola Tinubu

Barau ya jima ana fafatawa da shi a siyasar Najeriya. Ya yi aiki a majalisar wakilai daga 1999 zuwa 2003 bayan dawowar mulkin dimokradiyya.

Ɗan asalin jihar Kano, Barau ya riƙe muƙamai daban-daban kuma a yanzu shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa.

3. Opeyemi Bamidele

Sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Tsakiya, Opeyemi Bamidele, shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa.

Wannan shi ne karo na biyu da sanatan ya shiga majalisar dattawa bayan nasarar farko da ya samu a zaɓen 2019.

4. Lola Ashiru

Lola Ashiru na ɗaya daga cikin shugabannin majalisar dattawa, yana wakiltar Kwara ta Kudu kuma shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye.

A watan Agustan 2018 Lola Ashiru da wasu ƙusoshin PDP a Kwara suka sauya sheka zuwa APC domin yaƙar Bukola Saraki, wanda suke ganin ya kwashe shekaru 16 yana mulkin jihar.

5. Tahir Monguno

Sanata na gaba shi ne Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa, kwanan nan sanatocin APC suka zaɓe shi a matsayin mai tsawatarwa a majalisa bayan sauke Ali Ndume

Kara karanta wannan

Nenadi Usman: An naɗa mace a matsayin shugabar jam'iyya ta ƙasa a Najeriya

APC ta zargi Ndume da yi mata zagon ƙasa bayan sukar da ya yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Daga baya Ndume ya sasanta da jam'iyyar har an gan shi ya gana da Ganduje.

Sauran manyan sanatoci 5

S/NSunan SanatociMazaɓuMatsayi
6Nwebonyi Peter OnyekaEbonyi ta ArewaMataimakin mai tsawatarwa
7Abba MoroBenuwai ta Arewa maso GabasShugaban marasa rinjaye
8Akogun Lere OyewumiOsun ta YammaMataimakin shugaban marasa rinjaye
9Osita NgwuEnugu ta YammaMai tsawatarwa na marasa rinjaye
10Rufa'i HangaKano ta TsakiyaMataimakin mai tsawatar da marasa rinjaye

Majalisa ta gano masu riƙe tallafin Tinubu

A wani rahoton kuma majalisar dattawa ta bayyana takaicin yadda wasu yan kasar nan ke dakile yunkurin gwamnatin tarayya wajen tallafawa 'yan kasa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin ya ce gwamnati ta na iya kokarin tallafawa talakawa, amma daidaikun mutane suna hana ruwa gudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262