Gwamnan PDP Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar
- Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Gwamna Diri ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su shawo kan matsalar rikicin na PDP wanda ya ƙi ya ƙi cinyewa
- Gwamnan ya nuna cewa suna ƙoƙari domin warware rikicin saboda babu dimokuraɗiyyar da ke wanzuwa ba tare da adawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan rikicin shugabancin da jam’iyyar PDP ke fama da shi.
Gwamna Diri ya ce jam'iyyar PDP ta kasance jam'iyyar adawa mafi girmi a Najeriya kuma za ta magance ƙalubalen da ta ke fuskanta sannan ta sake komawa kan karagar mulki a ƙasar nan.
Ya kuma ba da tabbacin cewa jam’iyyar ba za ta ruguje ba, domin ba a yin mulkin dimokuradiyya ba tare da adawa ba, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Diri ya magantu kan rikicin PDP
Sanata Duoye Diri ya bayyana haka ne a yayin taron jam’iyyar PDP na jihar a cibiyar al’adu ta Gabriel Okara da ke birnin Yenagoa a ranar Asabar.
"Muna ƙoƙarin warware rikicin shugabanci na jam'iyyar mu a matakin ƙasa. Wannan jam'iyyar ba za ta ruguje ba. Ba a yin dimokuraɗiyya ba tare da adawa ba."
"Jam'iyyar PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa, za ta ci gaba da taka wannan rawar har zuwa lokacin da za ta sake karɓar mulki."
Gwamna Diri ya yabawa mambobin jam'iyyar PDP na jihar bisa biyayyarsu da sadaukarwarsu domin gina jam'iyyar da ci gaban jihar.
Wike ya caccaki gwamnonin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya gargaɗi gwamnonin jam'iyyar PDP su guji tsoma baki a harkokin siyasar jihar Rivers.
Wike wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne kuma babban ƙusa a PDP, ya ce ba shi da shirin barin jam'iyyar saboda wani mutum ɗaya.
Asali: Legit.ng