Malami Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Iya Kayar da Shugaba Tinubu a Zaɓen 2027
- Primate Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki a babban zaɓe na gaba
- Fitaccen limamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya
- Ayodele ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi duk mai yiwuwa domin ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har tsawon shekaru takwas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babban limamin cocin evangelical, Primate Elijah Ayodele ya ce tilas ƴan adawa su haɗa maja idan suna son kayar da shugaban kasa, Bola Tinubu a 2027.
Primate Ayodele ya buƙaci ƴan adawa su ajiye banbanci, su haɗe kai wuri ɗaya sannan su tsayar da ɗan takara ɗaya tilo da zai gwabza a zaɓen shugaban ƙasa na gaba.
Malamin addinin kirista ya yi wannan furucin ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa kwanan nan a shafinsa na manhajar X watau Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele ya yi hasashen takarar Atiku
Idan baku manta ba Ayodele ya gargaɗi jam'iyyar PDP da kar ta sake ta yi kuskuren baiwa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar takara.
Limamin cocin ya ce idan PDP ta sake ba Atiku takara a 2027, to ta zama gawa domin ba za ta kai labari ba.
Malamin ya faɗi hanyar kifar da Tinubi
A wannan karon kuma fitaccen limamin ya ce dole sai ƴan adawa sun dunƙule wuri ɗaya sannan za su iya turmushe Shugaba Tinubu a akwatun zaɓe.
"Idan kuna son kayar da Tinubu dole sai kun haɗa kai. Haɗuwar ku wuri ɗaya ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓen 2027.
"Ku sani Bola Tinubi ba zai ɗauki lamarin da wasa ba, shi kansa ya shirya yaƙin, dole ku zauna ku lalubo dabaru masu ƙarfi don tunkarar 2027."
- Primate Ayodele.
Gwamnan Nasarawa ya gana da Ganduje
Kuna da labarin Gwamnan jihar Nasarawa ya ziyarci shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a hekdkwar jam'iyyar da ke Abuja.
Abdullahi Sule ya gargaɗi ƴaƴan APC su kyale Ganduje ya fuskanci abubuwan da ke gabansa, ka da su ɗauke masa hankali.
Asali: Legit.ng