"Ku Daina Takura Wa Ganduje," Gwamna a Arewa Ya Faɗi Darajar Shugaban APC Na Ƙasa
- Gwamnan jihar Nasarawa ya ziyarci shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje a hekdkwar jam'iyyar da ke Abuja
- Abdullahi Sule ya gargaɗi ƴaƴan APC su kyale Ganduje ya fuskanci abubuwan da ke gabansa, ka da su ɗauke masa hankali
- Gwamnan Sule ya ƙara da cewa shugaban APC na ƙasa uban kowane kuma ya cancanki a girmama shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamma Abdullahi Sule na Nasarawa ya gargaɗi ƴaƴan APC su bar shugaban jam'iyyar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tunkari abubuwan da ke gabansa.
Gwamna Sule ya yi kashedin cewa bai kamata ƴaƴan APC su raba hankalin Ganduje ba a daidai lokacin da jam'iyyar ke tunkarar zaɓen gwamna a jihohin Edo da Ondo.
Abdullahi Sule ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya ziyarci Ganduje da sauran ƴan kwamitin gudanarwa (NWC) a hedkwatar APC da ke Abuja, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya girmama Ganduje
Gwamnan ya ce duba da abubuwan da ke faruwa a cikin APC, bai kamata ƴaƴam jam'iyyar su takurawa Ganduje da sauran ƴan kwamitin NWC ba.
Abdullahi Sule ya ce:
"Na zo nan ne domin kawo gaisuwa ga mutumin da ya cancanci girmamawa, shugabanmu na APC Ganduje. Ya cancanci mu ba shi girma da haɗin kai musamman a wannan lokacin.
"Nan da wasu ƴan makonni muna da zaɓe a Edo, ba zamu so a ɗauke masa hankali ba domin muna fatan samun nasara a Edo, wannan ya sa na zo na ƙara masa kwarin guiwa."
Sule ya koka kan rikicin APC a Benuwai
Gwamna Sule wanda shi ne shugaban gwamnonin APC a Arewa ta Tsakiya ya tabbatar rikici ya ɓarke a APC a ɗaya daga cikin jihohin yankin watau Benue.
Ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen warware wannan rigima kuma suna fatan uwar jam'iyyar ta ƙasa za ta taimaka wajen sasanta rikicin APC a Benuwai, Punch ta rahoto.
Wani ɗan gani kashenin Ganduje a Kano, Yusuf Babel ya ce ya faɗawa wakilin Legit Hausa cewa dama shugaban Party ya cancanci a ba shi girma ko ba dan Allah ba.
"Mai girma shugaban jam'iyya ya wuce duk inda ake tunani, ina da yaƙinin gwamnan Nasarawa ba don siyasa ƴa faɗi wannan kalaman ba, ya fahimci kimar Ganduje ne kawai.
"Amma a nan Kano waɗannan masu jajayen hulunan ba su san girmama na gaba ba. Har yau na kan ji farin ciki idan na kalli matsayin da Allah ya ba Ganduje a ƙasar nan," in ji shi.
Atiku ya haɗu da Nuhu Ribaɗu a Abuja
A wani rahoton kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya haɗu da Nuhu Ribadu a wurin sallar Jumu'a tare da sauran Musulmi a Abuja.
Atiku dai babban jagoran adawa ne a Najeriya yayin da Nuhu Ribadu ke aiki tare da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai bada shawara kan tsaro.
Asali: Legit.ng